Yadda wani matashi ya halaka innarsa mai shekaru 99 akan zargin maita
Rundunar Yansandan jahar Ogun sun samu nasarar kama wani matashi dan shekara 29, Owolabi Folorunso Adewale ya halaka innarsa mai shekaru 99 a duniya, Ebunola Aroboto a gidanta dake layin Maraisa, cikin yankin Ago-Iwoye na jahar Ogun.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Owolabi ya bayyana cewa ya kashe Aroboto ne saboda yana zarginta da sa hannu cikin matsalolin da yake fama dasu a rayuwarsa, inda yace ta kware wajen aika masa da ayyukan asiri da tsafe tsafe don kada ya cigaba.
KU KARANTA: Sarakunan gargajiya sun kai ma Buhari gaisuwar jinjina da ban girma a Villa
Kaakakin Yansandan jahar, Abimbola Oyeyemi ne ya tabbatar da kama Owolabi a ranar Talata, inda yace sun samu kira ne daga wasu mazauna unguwar, inda yace samun rahoton keda wuya sai da DPO na yansandan Ago-Iwoye, Ade Adedoyin ya garzaya wajen da abin ya faru.
Isar Yansanda keda wuya suka yi kicibus da Owolabi dauke da addan da yayi amfani da ita wajen kashe tsohuwar tare da daddatsata, nan da nan suka amshe addan, sa’annan suka kamashi, inda suka yi awon gaba dashi zuwa caji ofis.
“Wanda ake tuhuma ya amsa laifin kisan tsohuwar da adda, inda yace ya dauki wannan mataki akanta ne saboda tana yi masa asiri, don haka ta hana rayuwarsa cigaba. A jawabinsa, yace shi ma’abocin buga cacae Baba Ijebu ne, amma a duk lokacin da yake ganin zai ci, sai ya fadi.
“Don haka yace tsohuwa Aroboto, wanda yaya take ga mahaifinsa ce take amfani da tsafe tsafe wajen kawo masa cikas a cacar da yake bugawa, zuwa yanzu an mika gawar matar zuwa dakin ajiyan gawarwaki dake asibitin Ijebu-Ode.” Inji sanarwar.
Daga karshe kaakakin yace kwamishinan Yansandan jahar, Ahmed Iliyasu ya umarni mataimakin kwamishina mai kula da binciken manyan laifuka da tattara bayanan sirri, Wale Abass daya kaddamar da shirye shiryen shigar da Owolabi gaban kotu.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng