"Saura Ƙiris:" Trump Ya Faɗi Lokacin Kawo Ƙarshen Yaƙi da Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazana da cewa karfin sojin ƙasarsa shi ne mafi girma a dukkanin faɗin duniya
- Donald Trump ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke bayyana cewa yakin da ƙasarsa ke yi da Iran na tafiya cikin sauƙi
- Ana sa ran sabon zagayen tattaunawa tsakanin Amurka da Iran nan gaba kaɗan, inda ake ganin Trump zai iya zuwa da kansa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States – Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana kwarin gwiwa a yaƙin da ake yi da Iran inda ya ce komai ya tafiya sumul.
Wannan furuci nasa ya yi kama da irin hasashen da ya dade yana yi tun bayan da Amurka tare da Isra’ila suka kaddamar da hare-hare kan Iran a ƙarshen watan Fabrairu, 2026.

Source: Getty Images
Al-Jazeera ta wallafa cewa a cikin jawabin nasa, shugaban ya jaddada cewa ƙarfin sojojin Amurka ne ya ba su damar samun wannan matsayi.
'Za a kawo ƙarshen yakin Iran' – Trump
CNBC ta wallafa cewa Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce ana sa ran yakin Iran zai zo ƙarshe a nan kusa-kusa.
Ya ce:
“Muna da mafi ƙarfi rundunar soja a ko ina cikin duniya.”
Sai dai duk da wannan kyakkyawan hasashe daga Trump, rahotanni da dama na nuna cewa har yanzu akwai rikice-rikice da rashin tabbas dangane da yadda yakin zai ƙare.
An samu wannan damuwa ne musamman duba da ci gaba da takun saka tsakanin ƙasashen da ke da hannu a lamarin, kamar Isra'ila.
Trump ya sanar da tsagaita wuta
Tun da farko a ranar Alhamis 16 ga watan Afrilu, 2026, Trump ya sanar da cewa Isra’ila da Lebanon sun amince da tsagaita wuta na kwanaki 10.

Kara karanta wannan
Shugaba Trump ya yi maganar lokacin kawo karshen yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
Duk da haka, Iran ta koka kan cewa Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a Lebanon duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da ita ma Amurka ta shiga.

Source: Getty Images
Haka kuma, Trump ya nuna yiwuwar sake gudanar da tattaunawa kai tsaye tsakanin jami’an Amurka da na Iran. A cewarsa, ana iya yin hakan wataƙila, ko mako mai zuwa.
Duk da kalaman Trump, masana na ganin cewa makomar wannan rikici zai dogara ne kan yadda bangarorin da ke rikicin za su ci gaba da tattaunawa da kuma mutunta yarjejeniyoyin tsagaita wuta.
Shugaban Amurka ya magantu kan Iran
A baya, mun wallafa labarin cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya dauko batun yarjejeniyar da aka shirin cimma wa tsakanin kasarsa da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Donald Trump ya nuna cewa Iran a shirye take ta yi abubuwan da watanni biyu da suka gabata ba za ta iya yinsu ba, musamman ta fuskar hana ta mallakar makamashin nukiliya.
Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa yana da kyakkyawan fatan cewa kasashen biyu za su cimma yarjejeniya domin kawo karshen yakin da aka fara a Fabarairun 2026.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
