Bakar muguwa: Wata tsohuwa ta yi ma jikarta ‘duren fiya fiya, ta aika ta barzahu
Rundunar Yansandan jahar Ogun ta sanar da kama wata mat yar shekara 42 mai suna Temitope Akinola biyo bayan zarginta da ake yi da kwankwada ma jaririyar diyarta fiya fiya bayan kwanaki biyu kacal da haihuwarta.
Jaridar The Cables ta ruwaito a ranar 21 ga watan Nuwamba ne Yansanda suka kama Akinola a garin Sagamun jahar Ogun, kamar yadda kaakakin Yansandan jahar, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar.
KU KARANTA: Kowa ya bar gida, gida ya bar shi: Atiku zai dawo Najeriya ranar da ya cika shekaru 73
Oyeyemi yace mahaifiyar jaririyar ta bar jaririyar ne a hannun kulawar babarta, inda ta shiga bandaki domin ta yi wanka, amma koda ta dawo, sai dai kawai ta tarar da gawar diyar kwance ba rai.
“Samun rahoton ke da wuya sai muka aika da jami’anmu zuwa gidan da lamarin ya auku, inda suka kama matar nan take, yayin da take amsa tambayoyi, ta bayyana mana cewa bata son saurayin da yarinyarta ke kokarin aura ne, wanda kuma shi ne uban jaririyar.
“Tun lokacin da diyar ke dauke da cikin jaririyar ta yi kokarin zubar da cikin, amma sai Faston cocinsu ya hanata, don haka sai ta bari sai da diyar ta haihu sa’annan ta aikata wannan aika aika, ta tabbatar da yin amfani da fiya fiyan ‘Sniper’ wajen kashe jaririyar.” Inji shi.
Daga karshe Oyeyemi yace sun mika gawar jaririyar zuwa dakin ajiyar gawa na asibitin koyarwa na jami’ar Olabisi Onabanjo dake Sagamu domin gudanar da bincike, yayin da suka mika kakar zuwa sashin binciken manyan laifuka domin gudanar da karin bincike.
A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jahar Osun ta sanar da kama wata mata mai suna Rukayat Abulraheem mai shekaru 33 a garin Osogbo, babban birnin jahar Osun biyo baya zarginta da ake yi da halaka dan cikinta.
Sai dai babu tabbataccen hujja da uwar ta bayar na aikata ma dan da ta haifa wannan aika aika, amma Yansanda sun bayyana matar ta kashe Abdulganiyu ne a ranar 17 ga watan Nuwamba ta hanyar hankada shi cikin rijiya.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng