40%-50% na mukamai na za su fada ne a hannun Mata – Gwamna Abiodun
Dazu nan mu ka samu labari daga Jaridar Vanguard cewa gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya yi alkawarin za a ga kusan 40% zuwa kashi 50% na mukaman da zai raba a hannun mata.
Prince Dapo Abiodun ya nuna cewa gwamnatinsa za ta tafi da mata domin sun mara masa baya a lokacin zabe. Gwamnan yace Matan za su yi samun rabin kaso a cikin gwamnatinsa zuwa rabi.
Gwamna Abiodun ya fito ya na cewa: “Ina so in tabbatar maku da cewa a gwamnatina, za a samu rabin mukamai a hannun mata, idan ba a samu wannan ba, akalla kashi 40% za su tafi hannunsu.”
Gwamnan zai ba matan tarin kujeru a gwamnati ne saboda su ne su ka yi sanadiyyar zamansa gwamna. Dapo Abiodun yake cewa zai shiga kowane lungu da sako wajen kason mukaman na sa.
Bayan haka, gwamnan ya bayyana cewa zai yi kokarin ganin ya tada hanyoyin shiyyar Yammacin Ogun. Gwamnan yace akwai bukatun a gyara wasu titin yayin da za a gina sababbi.
KU KARANTA: Gwamnan Bauchi ya yi karin haske game da rade-radin wata katabora
Gwamna Abiodun zai ba Yammacin jihar wannan muhimmanci ne saboda irin gudumuwar da su ke ba jihar. “Idan babu Yammacin Ogun, ba za mu zama jihar da mu ka zama a yau ba.” Inji sa.
Yankin Ogun ta yamma ne bangaren da ya fi ko ina morewa da karfin tattalin arziki a kaf Nahiyar Afrika. Wannan ya sa Dapo Abiodun yake ganin mutanen yankin sun cancanci a yi masu ayyuka.
“Za mu tabbata mun ba Mata fiye da 100, 000 bashi domin su samu jarin kasuwanci ba tare da sun bada wata jingina ba. Bashin kuma zai zo ba tare da karin kudin ruwa ba.” Inji gwamnan na APC.
Jiya kun ji cewa gwamna ya samu matsala da jama’an Gari saboda ya ba Bahaushe mukami. Nadin wani Hausa-Fulani a matsayin Kantoma ne ya jawowa Simon Lalong surutu da suka.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng