Trump Ya Sanar da Matsayar da Israila da Lebanon Suka Cimma kan Tsagaita Wuta
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kasashen Israila da Lebanon
- Donald Trump ya bayyana cewa ya yi magana da shugabannin kasashen biyu domin ganin an samu zaman lafiya
- Shugaban na Amurka ya yi alfahari da cewa ya magance yakoki tara a fadin duniya kuma wannan tsagaita wutar ta zama ta 10
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ƙasashen Isra'ila da Lebanon sun amince da tsagaita buɗe wuta.
Trump ya bayyana cewa kasashen biyu sun amince da jarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwanaki goma (10) wadda za ta fara aiki a yau Alhamis, 16 ga Afrilu, 2026.

Source: Getty Images
Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Alhamis, 16 ga watan Afirilun 2026.
Sai dai, babu wata alama da ke nuna cewa ƙungiyar Hezbollah da Iran ke goyon baya tana cikin wannan yarjejeniya..
Me Trump ya ce kan tsagaita wuta?
Trump ya bayyana cewa wannan tsagaita wuta ya biyo bayan tattaunawa ta "musamman" da ya yi da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kuma Shugaban Lebanon Joseph Aoun.
Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da Isra'ila da Lebanon suka gudanar da tattaunawar zaman lafiya a birnin Washington.
“Na kammala tattaunawa ta musamman da babban Shugaba Joseph Aoun na Lebanon, da kuma Firaminista Bibi Netanyahu na Isra’ila."
"Waɗannan shugabanni biyu sun amince cewa, domin samar da zaman lafiya tsakanin ƙasashensu, za su fara shirin tsagaita wuta na kwanaki 10 a hukumance da misalin ƙarfe 5:00 na yamma."
- Donald Trump
Lebanon da Isra'ila sun tattauna
Trump ya bayyana cewa a ranar Talata ƙasashen biyu suka haɗu a karon farko cikin shekaru 34 a Washington, tare da Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio.
Ya ce ya umarci mataimakin shugaban kasa JD Vance, Ministan harkokin waje, Marco Rubio, da kuma shugaban hafsoshin tsaro, Janar Dan ‘Razin’ Caine, da su yi aiki da Isra'ila da Lebanon domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Kara karanta wannan
Shugaba Trump ya yi maganar lokacin kawo karshen yaki da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
“Abin alfahari na ne da na magance yaƙoƙi tara a faɗin duniya, kuma wannan zai kasance na 10, don haka bari mu gama da wannan aikin!”
- Donal Trump

Source: Facebook
Hezbollah ta shiga yakin Iran
Shugaba Trump ne ya ƙaddamar da yaƙi a kan Iran tare da Isra'ila a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.
Daga baya ƙungiyar Hezbollah ta janyo Lebanon cikin wannan yaƙi na Gabas Ta Tsakiya ta hanyar harba makamai masu linzami zuwa Isra'ila domin nuna goyon baya ga Iran.
Tun daga wannan lokaci, hare-haren Isra'ila a Lebanon sun kashe fiye da mutane 2,000 tare da raba fiye da miliyan ɗaya da gidajensu, yayin da dakarun ƙasa na Isra'ila suka mamaye Kudancin ƙasar.
Ko da yake Trump ya ce Aoun da Netanyahu za su tattauna a ranar Alhamis, har yanzu babu wani tabbaci cewa wannan kiran ya gudana.
Trump ya kira sarkin Qatar
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya kira sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ta wayar tarho.
Rahotanni sun nuna cewa shugabannin biyu sun tattauna kan muhimman batutuwa musamman yakin Amurka/Isra'ila da Iran.
Sheikh Al Thani da Shugaba Trump sun yi duba tare da tattaunawa kan sababbin abubuwan da ke faruwa a yankin da ma duniya baki ɗaya sakamakon yakin Iran.
Asali: Legit.ng
