Farashin Kayan Abinci Ya Haura Sama yayin da ake Maganar Zaben 2027
- Cibiyar kididdiga ta kasa (NBS) ta fitar da rahoto game da farashin kayayyaki a watan Maris na shekarar 2026, inda ta nuna karuwar farashi
- A bayanin da ta yi, cibiyar NBS ta bayyana wasu nau'ukan kayan abinci da tashin farashinsu ya jawo karuwar tsadar kayayyaki a Najeriya
- NBS ta ambaci wasu jihohi da suka hada da Zamfara, Sokoto, Bauchi da sauransu da ta ce sun fi fuskantar matsalar hauhawar farashin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Cibiyar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashin doya, citta, rogo, gyada, makamashi da sufuri ne suka jawo tsadar kayayyaki zuwa kashi 15.38 a watan Maris, 2026.
A cikin rahotonta na wata-wata, NBS ta ce an samu tashin farashin dankalin turawa, tumatir da garin kwaki, wanda ya sa adadin ya tashi daga kashi 15.06 a watan Fabrairun 2026.

Source: UGC
Yadda farashi ya tashi a Najeriya
Daily Trust ta wallafa cewa rahoton NBS ya ce an samu tashin farashi da kashi 4.18 cikin 100 a watan Maris 2026, wanda ya fi na watan Fabrairu da tazarar kashi 2.17.
Wannan na nufin cewa a watan Maris 2026, saurin hauhawar farashin kayayyaki ya fi wanda aka samu a watan Fabrairu 2026.
Rahotanni sun nuna cewa yaƙin Amurka da Iran ya sa farashin danyen mai ya haura dala 100 kan kowace ganga, wanda hakan ya haifar da karin farashin man fetur, sufuri da kayan abinci.
Abubuwan da farashinsu ya fi tashi
NBS ta ce manyan abubuwan da hauhawar farashin ya fi shafa sun haɗa da kayan abinci da abubuwan sha (da ba giya ba), gidajen cin abinci, otel da sufuri.
Rahoton Vanguard ya nuna cewa abubuwan da farashin su bai tashi sosai ba sun haɗa da giya da taba sigari da kuma inshora da dai sauransu.

Kara karanta wannan
Ana shirin tafiya Hajji, an fara barazanar tsayar da aiki da jiragen sama a Najeriya
Jihohin da farashi ya fi tashi
A jihohi, NBS ta ce an samu mafi girman hauhawar farashi a Bayelsa (kashi 27.37), Sokoto (kashi 26.03) da Bauchi (kashi 23.67).
A daya bangaren kuma, jihohin da farashi bai tashi sosai ba a wannan karon sun hada da Osun (kashi 5.25), Kano (kashi 9.85) da Kaduna (kashi 10.38).
A wata-wata kuwa, rahoton ya ce farashi ya tashi a jihohin Zamfara (kashi 10.77), Bauchi (kashi 9.37) da Sokoto (kashi 9.05).
A daya bangaren kuma, jihohin da farashin wata-wata bai tashi sosai ba sun hada da Lagos (kashi 1.54), Akwa Ibom (kashi 1.80) da Rivers (kashi 1.89).

Source: Getty Images
Game da farashin abinci, farashi ya karu a Bayelsa (kashi 33.35), Sokoto (kashi 28.02) da Adamawa (kashi 21.67), Kano (kashi 4.29), Oyo (kashi 4.86) da Katsina (kashi 7.48).
Amma a farashin wata-wata, Sokoto (kashi 11.78), Niger (kashi 8.59) da Gombe (kashi 8.10), yayin da a Katsina ya tashi da (kashi 0.09), Ogun (kashi 0.77) da Adamawa (kashi 1.30).
Legit ta tattauna da dan acaba
Yayin da ake maganar tsadar farashin kayayyaki da sufuri, wani mai sana'ar acaba ya bayyana wa Legit cewa kafin fara yakin, suna sayen lita a kan N870 zuwa kasa ko sama da haka da kadan.
Muhammad Ibrahim ya ce:
"Bayan fara yakin sai da muka rika sayen lita a kan N1400 a wasu gidajen mai.
"Babban abin damuwa shi ne mutane ba su kara mana kudi. Idan kuma baka dauki mutum ba ma, wani zai dauke shi."
Magana kan farashin mai a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta yi magana kan tashin farashin man fetur da ya samu saboda yakin da ake a Gabas ta Tsakiya.
Ministan kudi na kasa, Wale Edun ya sanar da cewa babu shirin dawo da tallafin man fetur duk da korafin da ake a fadin kasar.
Edun ya kara da cewa abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne tallafawa masu karamin karfi ba wai rusa tsare-tsaren da aka kawo ba.
Asali: Legit.ng

