Hukumar yan sandan NAjeriya
Wata kotun majistri a jahar Ebonyi ta yanke hukuncin dauri na tsawon watanni 18 ga wani matashi mai shekaru 37, Obinna Nwankwo sakamakon kama shi da ta yi da laifin lakada ma uwarsa dan banzan duka.
Akalla mabiyan darikar Shia na kungiyar yan uwa Musulmai, watau Islamic Movement in Nigeria, IMN, ne suka samu munana rauni a sakamakon wata arangama da suka yi da jami’an rundunar Yansandan Najeriya a Abuja.
Wani barawo mai suna uche Akunacha mai shekaru 41 ya aikata ma kansa aika aika ta hanyar kashe kansa da kansa a lokacin da ya tafka tsalle daga gidan sama mai hawa biyu don ya tsere daga mutanen da ya yi ma sata.
Wasu gungun yan bindiga dadi sun kai ma jami’an rundunar Yansandan Najeriya hari a jahar Delta a yayin da suke aikin binciken motoci a shingen binciken ababen hawa dake cikin garin Asaba, babban birnin jahar Delta.
Wani mutumi da zarginsa da tabin hankali, Badejo Adewale ya banka ma wani abokin zaman sa, Bolatito Kadara wuta a unguwar Surulere na jahar Legas a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kafa bincike don gano sahihancin wani bidiyo da ya bayyana wanda ke nuna yadda wani jami’in ‘dan sanda ke amfani da na’urar cirar kudi ta POS wajen karbar cin hanci daga hannun wani mutumi.
Ke duniya, ina za ki da mu ne? wata kotun majistri dake zamanta a garin Abakaliki na jahar Ebonyi ta bada umarnin garkame wani matashi dan shekara 37, Chibueze Iduma a kan tuhumarsa da ake da kashe mahaifinsa.
Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Filato ta sanar da kisan wasu mutane 12 da ake zargin miyagun yan bindiga makiyaya ne suka halakasu a kauyen Kulben dake lardin Kombun cikin karamar hukumar Mangu na jahar.
Bidiyon wani jami’in dan sanda na nan yana yawo yanzu haka a kafofin watsa labarai. An zargi jami’in da neman a bashi cin hanci daga hannun Wani mutum.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari