Abin da Buhari Ya Nema a Wurin Sheikh Karibullah a Lokacin Yana Shugaban Kasa

Abin da Buhari Ya Nema a Wurin Sheikh Karibullah a Lokacin Yana Shugaban Kasa

  • Sheikh Karibullah Nasiru Kabara ya bayyana irin dangantakar da ke tsakanin marigayi Muhammadu Buhari da malamai, musamman ta bangaren tunatar da shi
  • Fitaccen malamin addinin Musulunci ya bayyana alakarsa da Buhari a ranar Litinin 13 ga watan Yuli, 2026 a taron tuna wa da tsohon shugaban kasar
  • Sheikh Karibullah, wanda shi ne jagoran darikar Kadiriyya ya ce ya kan zauna daga shi sai Muhammadu Buhari sai Allah domin yi masa nasiha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara, ya bayyana irin dangantakar da ta kasance tsakaninsa da marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da kuma yadda yake ba shi shawarwari a lokacin da yake mulki.

Malamin ya bayyana hakan ne a taron cika shekara guda da rasuwar Buhari, wanda ya rasu a shekarar 2025 bayan gajeriyar rashin lafiya a wata ƙasar waje.

Kara karanta wannan

Taron tuna Buhari: Tinubu, Gowon, Shettima, Zulum da sauransu sun magantu

Sheikh Karibullah ya tuna alakarsa da Buhari
Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, Muhammadu Buhari Hoto: Sheikh Qaribullah Nasir Kabara/Muhammadu Buhari
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Sheikh Karibullah ya ce yana cikin malaman addinin Musulunci da Buhari ya ba wa dama su riƙa tunatar da shi abin da Allah (SWT) Ya umarta.

Buhari ya ba ni dama - Karibullah Kabara

Sheikh Karibullah Nasiru Kabara ya ce Buhari ya ba shi dama ya riƙa sanar da shi duk lokacin da ya ga wani abu da zai amfani ƙasa ko kuma ya dace da amanar da yake ɗauke da ita.

A cewarsa:

"Ya ba ni wata dama na cewa duk sanda na hango wani abu da zai zama alkhairi ga wannan amanar da yake ɗauke da ita, ko Allah Ya so na nuna masa ita, na sanar da shi."

Malamin ya ƙara da cewa sau da dama yakan zauna shi kaɗai da Muhammadu Buhari, inda yake ba shi shawarwari kan abubuwan da ya ga sun dace.

Na zauna da Buhari - Sheikh Karibullah

Kara karanta wannan

Adeyemi: 'Yadda na samo aron N400m wajen kafa hukumar bogi

Sheikh Karibullahi Nasiru Kabara ya kara da cewa ya rika zama da Muhammadu Buhari daga shi, sai tsohon shugaban kasa, sai Allah SWT.

Karibullah ya ce Buhari ya kan nemi a rika yi masa nasiha
Marigayi Buhari a ofis a lokacin yana shugaban kasa Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

A kalamansa:

"Alhamdulillah, mun ci gaba da yin wannan. Idan na ga wani abu da ya kamata na ba shi shawara a kai, ko gyara, ko wani abu da ya kamata, na kan yi masa shawara."

Ya ƙara da cewa:

"Kuma sau da yawa ma mu kan zauna daga ni sai shi sai Allah."

Fitaccen malamin na daga cikin gomman mutane da suka halarci taron cika shekara guda na rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da aka yi a Abuja.

A wajen taron tunawa da marigayi Buhari, matar tsohon shugaban kasa, Aisha Buhari, 'ya'yansa, abokan arzikinsa, jami'an gwamnati da sauran al'umma sun halarta a babban birnin tarayya, Abuja.

Aisha Buhari ta kaddamar da gina dakin karatu

A baya, mun wallafa cewa matar tsohon shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta bayyana wasu daga cikin manyan abubuwan da Muhammadu Buhari ya bar wa Najeriya, musamman ta fuskar ilimi.

Kara karanta wannan

Mijin dalibar Ma'un ya zayyano abin da ya faru tsakaninsu da malamin jami’a a Kano

Ta bayyana yadda tsohon shugaban ya yi tsayin daga wajen tabbatar da ingancin ilimi a Najeriya a yayin da ta kaddamar da aikin gina kwalejin kimiyyar kwanfuta a Jami'ar Al-Qalam da ke Katsina .

An assasa samar da wannan bangare ne domin tuna wa da kokarin da Muhammadu Buhari ya yi a kan ilimi da kuma niyyar zai taimaka wajen bunkasa ilimin zamani a jami'ar da ma jihar Katsina baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng