An sake kwatawa: Miyagu sun kai hari jahar Nassarawa, sun kashe mutane 4

An sake kwatawa: Miyagu sun kai hari jahar Nassarawa, sun kashe mutane 4

Yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun kai wani mummunan samame a unguwar Abebe dake cikin karamar hukumar Keana na jahar Nassarawa, inda suka kashe mutane hudu babu laifin fari balle na baki.

Daily Trust ta ruwaito baya ga kashe mutane hudu, makaharan sun raunata wasu mutane biyu sakamakon harbin bindiga. Wani daga cikin wadanda suka tsallake harin, Vitalis Adam ya bayyana wadanda suka mutu kamar haka.

KU KARANTA: Turi ya kai bango: Mutanen gari sun yi fito na fito da yan bindiga, sun kashe 5 a Filato

“Wani jami’in Cocin St Augustine, Augustine Avertse da mahaifinsa Avertse Akaa’am, Uwongul John Akodi da kuma wani mutumi mai suna Monday, yan bindigan sun harbe su ne yayin da suke kokarin tserewa cikin daji.” Inji shi.

Adams yace shi da wani Mista Friday Gboko sun sha da kyar a lokacin da suka shige cikin daji, amma duk da haka sai da harsasan yan bindigan suka ji musu rauni daban daban a jikkunansu, kuma a yanzu haka suna samun kulawa a asibitin garin Obi.

Sai dai a jawabinsa, Adams ya danganta harin da kokarin yan bindigan na yi ma wani manomi fashin kudinsa N200,000 daya dawo dasu gida bayan ya ci kasuwa inda ya sayar da kayayyakin amfanin gonarsa.

Da majiyarmu ta tuntubi kaakakin rundunar Yansandan jahar Nassarawa, ASP Rahman Nansel game da harin, sai yace rundunarsu bata samu rahoton harin ba.

A wani labarin kuma, wasu gungun yan bindiga da suka fitini al’ummar karamar hukumar Kanam da fashi da makami sun gamu da ajalinsu a hannun ayarin fusatattun jama’an gari da suka yi fito na fito dasu ba tare da jin tsoro ba.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa isarsu garin keda wuya sai jama’an kauyen suka samu labarin cewa mutanen nan yan fashi ne, domin kuwa sun tare wata motar kamfanin taliya kirar Toyota Bus a kan hanyar Wase-Kanam, suka kwace N1.5m.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel