Mai rangwamen hankali ya jika makwabcinsa da fetur, ya banka masa wuta

Mai rangwamen hankali ya jika makwabcinsa da fetur, ya banka masa wuta

Wani mutumi da ake zarginsa da tabin hankali, Badejo Adewale ya banka ma wani abokin zaman sa, Bolatito Kadara wuta a unguwar Surulere na jahar Legas a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Badejo ya aikata hakan ne a gidansu mai lamba 13, a kan titin Aiyeleto dake unguwar Surulere, inda ya jika abokin zamansa sharkaf da man fetir, sa’annan ya banka masa wuta.

KU KARANTA: Badakalar $24000: Ba zan taba yin shiru wasu na fadin karairayi a kai na ba – Shehu Sani

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mai magana da yawun rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Legas, Bala Elkana ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace mahaukacin ya wawwatsa ma Kadara fetir, daga nan sai ya cinna masa wuta.

Kaakaki Elkana yace yar uwar wanda aka kona, Adeola Kadara ce ta kai musu kara zuwa ofishin Yansanda dake Surulere inda ta shaida ma jami’an Yansanda cewa ta samu labarin an banka ma dan uwanta wuta.

“A yanzu haka mun zarce da shi zuwa babban asibitin tsibirin Legas, kuma ya fara farfadowa, ya shaida ma Yansanda yadda Adewale, wanda ke da ciwo tabin hankali ya watsa mai fetir, sa’anann ya cinna masa wuta.

“Yansanda sun cigaba da gudanar da bincike a kan Adewale har zuwa dakin da aka kwantar da shi a asibitin mahaukata dake Yaba a jahar Legas.” Inji Elkana.

Sai dai kaakaki Elkana yace duk kokarin da aka yi na jin ta bakinsa ya gagara sakamakon baya magana, ya ki cewa uffan, amma dai yace ba zasu yi kasa a gwiwa ba wajen cigaba da gudanar da bincike.

A wani labarin kuma, Y’ayan babbar kungiyar yan Shi’a a Najeriya, watau kungiyar yan uwa Musulmi ta Najeriya, IMN, sun yi kira tare da jaddada gargadi ga gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, inda suka ce masa ya kiyayi ranar sakamako.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel