PFIPC: Yadda 'Yan Sanda Suka Bankado Ma'aikatar Bogi a Karkashin Gwamnatin Tinubu
- Rahoton wucin gadi na 'yan sanda ya ce ya gano yadda aka kirkiri wata hukumar gwamnati mai suna PFIPC
- Ana zargin Prince Adeniyi Adeyemi Mathew da gabatar da kansa a matsayin darakta janar na hukumar da ba ta wanzu
- Binciken na 'yan sanda ya bayyana cewa PFIPC ba ta cikin kowace doka ko tsarin gwamnatin tarayyar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani rahoton wucin gadi na binciken 'yan sanda ya bayyana yadda jami'ai suka bankado ayyukan hukumar PFIPC.
Rahoton ya nuna cewa ana amfani da takardun bogi wajen gudanar da ayyuka da sunan hukumar PFIPC wadda gwamnati ba ta san da ita ba.

Source: Twitter
Rahoton ya ce binciken ya fara ne bayan ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa ya kai koke ga Sufeto Janar na 'yan sanda a ranar 17 ga Oktoban 2025, jaridar Vanguard ta kawo labarin.
Abin da binciken farko ya gano
Rahoton ya bayyana cewa takardun da ake zargi na bogi sun kunshi sa hannu, lambobi, hatimin gwamnati da kuma tambarin Najeriya da aka kirkira.
A cewar rahoton, an yi amfani da wadannan takardu wajen nada mutane mukamai a cikin PFIPC, wadda binciken ya ce ba ta da wata shaidar kasancewa a hukumance.
Wanda ake zargi da jagorantar lamarin
Masu bincike sun bayyana babban wanda ake zargi a matsayin Prince Adeniyi Adeyemi Mathew, wanda ake zargin ya rika gabatar da kansa a matsayin shugaban PFIPC.
Rahoton ya ce yana gudanar da aiki daga wani ofishi da ke cikin Federal Secretariat Complex, Phase III, Abuja, inda ake zargin ya rika ganawa da 'yan Najeriya da baki tare da bayyana kansa a matsayin shugaban wata hukumar gwamnati.
Haka kuma, ana zargin ya rubuta wasika zuwa ma'aikatar harkokin wajen Najeriya yana neman a aika da bukatar 'Note Verbale' zuwa ofishin jakadancin Amurka domin saukaka neman bizar wasu da ya bayyana a matsayin ma'aikatan PFIPC.

Kara karanta wannan
PFIPC: Shugaban hukumar bogi ya soki binciken ICPC, ya aika sako ga Shugaba Tinubu
Kamu da binciken da aka gudanar
'Yan sanda sun ce an kama Adeyemi a ranar 27 ga Oktoban 2025 a ofishin da ake zargin yake gudanar da ayyukansa.
Bayan kama shi, jami'ai sun gudanar da bincike a ofishin da kuma gidansa da ke APC Quarters, Suleja, jihar Neja, bisa sammacin kotu.
A cewar rahoton, an kwato takardun bada mukamai da ake zargin na bogi ne, takardun hukuma, wasiƙu zuwa ma'aikatu, sassa da hukumomin gwamnati (MDAs), da sauran kayayyakin da ake ganin suna da muhimmanci ga binciken.
Abin da wanda ake zargin ya fada
A bayaninsa ga masu bincike, ana zargin Adeyemi ya ce wani Dolapo Babatunde Tanimola ne ya taimaka masa wajen samun takardar nadin da ta bayyana shi a matsayin shugaban PFIPC.
Sai dai 'yan sanda sun ce daga baya bincike ya nuna cewa Tanimola ya rasu a wata gobara da ta tashi a Kachi Hotel, Utako, Abuja, tun kafin a kama Adeyemi.
Karin bincike kan lamarin
A wani bangare na binciken, 'yan sanda sun tuntubi Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya domin samun sahihin kwafin takardar nadin da ake magana a kai.
Har ila yau, an gayyaci jami'ai daga Ofishin Akanta Janar na Tarayya domin yi musu tambayoyi.
Rahoton ya ce ma'aikata uku da aka tura daga ofishin Akanta Janar zuwa ofishin PFIPC sun shaida wa masu bincike cewa an tura su can tun ranar 28 ga Agustan 2025, amma ba su gudanar da wani aiki na hukuma ba a tsawon lokacin da suka kasance a wurin.

Source: Facebook
Binciken asusun banki
Binciken harkokin kudi da aka gudanar tare da hadin gwiwar hukumar NFIU ya nuna cewa ana zargin Adeyemi yana gudanar da asusun banki guda 34 masu aiki a bankunan kasuwanci daban-daban.
A karshe, rahoton 'yan sanda ya ce bincikensu ya tabbatar da cewa PFIPC wata hukuma ce kirkirarra wadda ba ta cikin kowace doka ko tsarin gwamnatin tarayyar Najeriya, kuma ba a amince da ita a hukumance ba.
Adeyemi ya aika wasika ga Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Adeniyi Adeyemi da ke ikirarin shugabantar hukumar PFIPC ya aika da wasika ga Shugaba Bola Tinubu.
Adeniyi Adeyemi ya bukaci mai girma Bola Tinubu da ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gano gaskiya kan lamarin.
Asali: Legit.ng

