Duniya ina za ki da mu? Matashi ya lakada ma mahaifiyarsa dan banzan duka a jahar Ebonyi

Duniya ina za ki da mu? Matashi ya lakada ma mahaifiyarsa dan banzan duka a jahar Ebonyi

Wata kotun majistri a jahar Ebonyi ta yanke hukuncin dauri na tsawon watanni 18 ga wani matashi mai shekaru 37, Obinna Nwankwo sakamakon kama shi da ta yi da laifin lakada ma uwarsa dan banzan duka.

Jaridar The Nation ta ruwaito baya ga casa uwarsa mai suna Chinyere Nwankwo, matashin ya yi mata asara da ta kai ta naira dubu 160 bayan ya kakkarya mata kujerun roba, tagogi da sauran kayayyaki masu amfani a gidanta.

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 7 game da sabon gwamnan jahar Imo, Hope Uzodinma

A zaman kotun na ranar Talata, Obinna ya amsa aikata tuhume tuhume guda biyu da Yansanda suke masa da suka hada da cin zarafin babarsa da kuma barnatar da kaya ba bisa hakki ba, daga nan ne Alkalin kotun, mai sharia Happines Chima ta yanke masa hukuncin wata 18 a kurkuku.

A cewar Alkaliyar, ta yanke masa wannan tsatstsauran hukunci ne ba tare da zabin biyan tara ba saboda ya ci mutuncin babarsa wanda ta yi dawainiyarsa tsawon watanni 9 a cikin cikinta, ta kara da cewa wannan cin mutunci ne ga matan duniya gaba daya.

Da fari sai da Dansanda mai kara, Inspekta Chinedu Mbam ya bayyana ma kotun cewa da misalin karfe 6 na yammacin ranar 11 ga watan Janairu ne Obinna ya buga ma babarsa karfen rodi a kai da gangan, inda yace laifin ya saba ma sashi na 351 da 451 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Ebonyi.

A wani labari kuma, wani dalibin sakandari ya shiga hannun bayan ya kashe malaminsa ta hanyar caka masa wuka har sau biyu a kirjinsa a ranar Talata, 14 ga watan Janairu a makarantar sakandari ta Nkolbisson dake Yaounde, babban birnin kasar Kamaru.

Daliban makarantar sun bayyana cewa tun a ranar Litinin aka fara samun takun saka tsakanin malamin da wannan dalibi da ba’a bayyana sunansa ba. Daliban sun ce a ranar Talata ne dalibin ya shiga aji, inda ya zabga ma malamin mari, sa’annan ya caka masa wuka a kirji.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel