Tsuguni bata kare ba: Miyagun yan bindiga sun halaka mutane 12 a jahar Filato

Tsuguni bata kare ba: Miyagun yan bindiga sun halaka mutane 12 a jahar Filato

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Filato ta sanar da kisan wasu mutane 12 da ake zargin miyagun yan bindiga makiyaya ne suka halakasu a kauyen Kulben dake lardin Kombun cikin karamar hukumar Mangu na jahar.

Rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta bayyana cewa yan bindigan sun jikkata wani mutum, kamar yadda mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar, DSP Terna Tyopev ya tabbatar a garin Jos.

KU KARANTA: Tirka tirkan IPPIS: Kungiyar malaman jami’a ta yi ganawar sirri da shugaban Buhari a Villa

Tyopev ya ce: “Da tsakar daren Alhamis, 9 ga watan Janairu ne muka samu kiranye daga jama’a cewa yan bindiga sun kai farmaki kauyen Kulben, kuma suna zargin yan bindiga makiyaya ne, a sakamakon wannan hari mutane 12 sun mutu, guda kuma ya samu mummunan rauni.”

DSP Tyopev ya bayyana cewa tuni an garzaya da wanda ya jikkatan zuwa babban asibitin garin Mangu ana duba lafiyarsa, don haka ya yi kira ga jama’an garin da su kwantar da hankulansu kuma su zauna lafiya tare da kansancewa masu bin doka da oda, inda ya tabbatar musu da cewa jam’an tsaro na iya kokarinsu don ganin sun kamo yan bindigan.

“Zuwa yanzu dai bamu kama kowa ba, amma muna yin iya kokarinmu don ganin mun kamo wadanda suka aikata wannan aika aika tare da tabbatar sun fuskanci hukuncin daya dace dasu.” Inji shi.

Daga karshe Kaakakin Tyopev ya yi kira ga jama’a dasu baiwa Yansanda bayanan sirri masu amfani da zasu taimaka musu wajen bin sawun yan bindigan.

A wani labarin kuma, gungun yan bindiga sun kaddamar da hari a garin Beni dake cikin karamar hukumar Neja, inda suka yi awon gaba da babban limamin Masallacin Juma’an garin, Malam Umar Muhammad, tare da wasu mutane 20.

Rahotanni da dama sun bayyana cewa yan bindigan da yawansu ya kai 50 sun yi ta shiga kauyuka daban daban ne suka yi ma jama’a fashi, tare da kwashe shanunsu, daga nan suka afka Beni da Kudami na karamar hukumar Paikoro, a ranar Laraba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel