Adeyemi: Shugaban Ma'aikatar Bogi Ya Aika Wasika ga Tinubu ana Batun Kai Shi Kotu

Adeyemi: Shugaban Ma'aikatar Bogi Ya Aika Wasika ga Tinubu ana Batun Kai Shi Kotu

  • Adeniyi Adeyemi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa kan rikicin PFIPC
  • Ya bukaci kwamitin ya kunshi kungiyoyin fararen hula, kafafen yada labarai masu zaman kansu da wakilan kasashen duniya
  • Adeyemi ya ce ba zai mika kansa ba a karkashin halin da ake ciki saboda yana ikirarin akwai barazana ga rayuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Adeniyi Adeyemi, wanda ke ikirarin shi ne shugaban hukumar da ake takaddama a kanta mai suna Presidential Foreign Investment Promotion Council (PFIPC), ya aika sako ga Shugaba Bola Tinubu.

Adeniyi Adeyemi ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin binciken rikicin da ya dabaibaye hukumar.

Adeyemi ya aika wasika ga Tinubu
Adeniyi Adeyemi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne a wata budaddiyar wasika da ya aikewa shugaban kasa, a ranar Litinin, 13 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Adeyemi: 'Yadda na samo aron N400m wajen kafa hukumar bogi

Adeyemi ya ce wajibi ne kwamitin ya kasance mai cikakken 'yanci kuma ya kunshi bangarori daban-daban domin tabbatar da cikakken adalci da rashin nuna son rai.

Wadanda Adeyemi ya ce su shiga kwamitin

A cewarsa, ya kamata a zabo mambobin kwamitin daga kungiyoyin fararen hula, wakilan kafafen yada labarai masu zaman kansu, masu sa ido kan harkokin kudi na kasa da kasa da kuma kungiyoyin kare hakkin bil'adama kamar Amnesty International domin sa ido kan bin ka'idojin doka da na kasa da kasa.

Ya kuma ce ya dace a hada da wakilan Majalisar Dinkin Duniya (UN), Amurka, Birtaniya, Tarayyar Turai (EU), kungiyar ECOWAS da Tarayyar Afirka (AU).

Hakazalika, Adeyemi ya bukaci a sanya hukumomin yaki da cin hanci na ICPC da EFCC a matsayin abokan aiki a cikin wannan hadakar mai zaman kanta, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Dalilin kin amincewa da binciken ICPC

Tun da farko, Shugaba Tinubu ya umarci ICPC ta binciki lamarin. Sai dai Adeyemi ya ce kasancewar hukumar tana karkashin gwamnati, ba zai dace ta gudanar da bincike kan zarge-zargen da suka shafi bangaren gwamnati ba.

Kara karanta wannan

PFIPC: Shugaban hukumar bogi ya soki binciken ICPC, ya aika sako ga Shugaba Tinubu

"Idan ana son wannan bincike ya samu cikakkiyar amincewa daga 'yan Najeriya da kuma kasashen duniya, dole ne ya wuce iyakokin tsarin binciken gwamnati na yau da kullum."
"Da zarar an kafa wannan kwamitin mai zaman kansa da ya kunshi bangarori daban-daban, zan gabatar da cikakkun takardu da hujjojin da za a iya tantancewa. Ba zai yiwu tsarin da ake zargi ya binciki kansa cikin sahihanci ba idan manyan wadanda ake zargi suna cikinsa ba."

- Adeniyi Adeyemi

Adeniyi ya mika bukatarsa ga Tinubu
Adeniyi Adeyemi ya yi tagume zaune a cikin ofis Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew
Source: Facebook

Ya ce rayuwarsa na cikin hadari

Adeyemi ya kuma yi ikirarin cewa ba zai iya mika kansa ga hukuma a karkashin tsarin da ake ciki ba saboda yana fargabar kashe shi.

"Na samu sahihan bayanan sirri masu inganci da ke nuna cewa ana shirin kashe ni da zarar na bayyana a wurin da babu cikakken sa ido."

- Adeniyi Adeyemi

Ya kara da cewa wannan ba zato ko hasashe ba ne, yana mai cewa abin da ya faru da Dolapo Babatunde Tanimola, wanda ya bayyana a matsayin daya daga cikin manyan masu shiga tsakani a wannan batu, ya kara tabbatar masa da wannan fargaba.

Kara karanta wannan

Soke zabubbukan ADC: Atiku ya aika sako ga magoya bayan jam'iyyar kan zaben 2027

Za a gurfanar da Adeyemi gaban kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta shirya gurfanar da Adeniyi Adeyemi, wanda ke ikirarin shi ne shugaban hukumar PFIPC, wadda gwamnati ta ce ba ta san da ita ba.

Rundunar 'yan sandan za ta gurfanar da Adeniyi Adeyemi ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Talata, 14 ga watan Yulin 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng