Bidiyon wani dan sanda rike da POS inda ya bukaci wani matashi ya bashi ATM dinsa

Bidiyon wani dan sanda rike da POS inda ya bukaci wani matashi ya bashi ATM dinsa

- An gano wani jami’in dan sanda a kamara yana neman a bashi cin hanci

- An gano jami’in dauke da na’urar POS inda ya bukaci mutumin da ya bashi katin ATM dinsa

- Lamarin mai ban al’ajabi ya afku ne a bakin wani hanya mai yawan jama’a

Bidiyon wani jami’in dan sanda na nan yana yawo yanzu haka a kafofin watsa labarai. An zargi jami’in da neman a bashi cin hanci daga hannun Wani mutum.

Bidiyon wanda ya yi fice ya nuno dan sandan da ba a san kowanene ba rike da na’urar POS a hannunsa yayinda ya damke mutumin.

An jiyo jami’in cikin daga murya yana neman mutumin ya bashi katin ATM dinsa.

Sai dai dan sandan bai bayyana abunda yake niyan yi da ATM din ba sannan an kuma jiyo mutumin yana hana shi katin.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa ta’adanci zai cigaba a arewa maso gabas – Ndume

Koda dai dan sandan bai bayyana kudirinsa na kasancewa dauke da POS ba, yan Najeriya sun yi hasashen cewa yana kokarin karban cin hanci ne daga mutumin ta karfi da yaji.

Wani mai suna Kelechi Marshall ne ya yada bidiyon a shafin Twitter.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel