Rundunar yan sanda ta fara binciken bidiyon 'dan sanda mai POS

Rundunar yan sanda ta fara binciken bidiyon 'dan sanda mai POS

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kafa bincike don gano sahihancin wani bidiyo da ya bayyana wanda ke nuna yadda wani jami’in ‘dan sanda ke amfani da na’urar cirar kudi ta POS wajen karbar cin hanci daga hannun wani mutumi.

Rundunar ta bukaci duk wani mai bayanai kan lamarin da ya taimaka ya tuntubeta ta shafin pressforabuja@police.gov.ng

Babban sufeto Janar na ‘yan sandan kasar, Mohammed Adamu, ya yi tur da karbar cin hanci a tsakanin ma’aikatan gwamnati musamman ‘yan sanda.

Ya kuma ce rundunar a shirye take ta hukunta duk wani jami’i da aka samu da hannu a cin hanci da rashawa.

A baya mun ji cewa Bidiyon wani jami’in dan sanda na nan yana yawo yanzu haka a kafofin watsa labarai. An zargi jami’in da neman a bashi cin hanci daga hannun Wani mutum.

Bidiyon wanda ya yi fice ya nuno dan sandan da ba a san kowanene ba rike da na’urar POS a hannunsa yayinda ya damke mutumin.

An jiyo jami’in cikin daga murya yana neman mutumin ya bashi katin ATM dinsa.

KU KARANTA KUMA: ASUU ta fadi warwas bayan shugaba Buhari ya tilasta suyi rijista da IPPIS

Sai dai dan sandan bai bayyana abunda yake niyan yi da ATM din ba sannan an kuma jiyo mutumin yana hana shi katin.

Koda dai dan sandan bai bayyana kudirinsa na kasancewa dauke da POS ba, yan Najeriya sun yi hasashen cewa yana kokarin karban cin hanci ne daga mutumin ta karfi da yaji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel