An yi asarar haihuwa: Matashi ya kashe mahaifinsa saboda rikici a kan Doya a Ebonyi

An yi asarar haihuwa: Matashi ya kashe mahaifinsa saboda rikici a kan Doya a Ebonyi

Ke duniya, ina za ki da mu ne? wata kotun majistri dake zamanta a garin Abakaliki na jahar Ebonyi ta bada umarnin garkame wani matashi dan shekara 37, Chibueze Iduma a kan tuhumarsa da ake da kashe mahaifinsa.

Wannan lamari ya faru ne a kauyen Amaefia Ngbo dake karamar hukumar Ohaukwu na jahar Ebonyi a ranar 20 ga watan Disamba, amma sai a ranar Alhamis, 9 ga watan Janairun 2020 aka gurfanar da shi gaban kotu.

KU KARANTA: Malaman jami’a sun ki cewa uffan bayan sun goga gemu da gemu da Buhari a Villa

Jaridar Punch ta ruwaito yaron da mahaifinsa, Mista Emmanuel Iduma sun samu matsala a tsakaninsu ne wanda ta kai ga rikici a kan wani doya da yaron ya dafa a gida, amma bayan ya dafa ya sauke, sai ya fita don ziyarar wani abokinsa.

Sai dai fitar yaron ke da wuya sai mahaifinsa ya shigo gidan, inda ya yi ido biyu da wannan dafaffen doya, ai kuwa ba tare da bata lokaci ba cinye doyan nan, amma ko da yaron ya dawo ya tarar babansa ya cinye doya, sai ya tunkari baban.

“Wannan shi ne musabbabin rikici a tsakaninsu, har ta kai ga mahafin ya dauki sandar da yake dogarawa ya buga ma yaron, abin ka da yaro mara tarbiyya, shi ma sai ya amshe sandan ya zabga ma baban nasa, abin ka da ajali kuma, nan take baban ya fadi matacce.” Inji Yansanda.

Dansandsa mai kara, Inspekta Chinedu Mbam ya shaida ma kotu cewa laifin da ake tuhumar yaron ya saba ma sashi na 319(1) na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Ebonyi. Sai dai lauya mai kare wanda ake kara ya nemi a bada belin sa.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu ne sai Alkali Blessing Chukwu ta zartar da cewa kotun ba ta da hurumin sauraron karar, don haka ta bada umarnin a daure matashin a gidan gyaran halaye na Najeriya, sa’annan a mika takardar tuhumar ga daraktan shigar da kara na jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel