Ba duka aka lalace ba: An karrama Dansandan da bai taba amsan cin hanci ba

Ba duka aka lalace ba: An karrama Dansandan da bai taba amsan cin hanci ba

A duk yadda al’umma ta kai ga lalacewa, ba’a rasa na kirki a cikinsu, hakan ya sake tabbata a kan wani jami’in rundunar Yansandan Najeriya wanda aka tabbatar da nagartarsa da har tasa ya ki karbar cin hancin kudi naira miliyan 6.

Jaridar Information Najeriya ta ruwaito wannan dansanda sunansa Francis Erhabor, shi ne DPO na Yansandan garin Itam na jahar Akwa Ibom, an taba masa tayin naira miliyan 6 a shekarar 2019 yayin da yake aiki a jahar Edo don a samu daman fasa bututun mai amma ya ki.

KU KARANTA: Za mu dawo da Diezani Allison Madueke gida Najeriya don ta fuskanci hukunci – Magu

Ba duka aka lalace ba: An karrama Dansandan da bai taba amsan cin hanci ba
Ba duka aka lalace ba: An karrama Dansandan da bai taba amsan cin hanci ba
Asali: Facebook

Asali ma abokan aikinsa sun tabbatar da cewa Dansanda Francis bai taba nema ko karban cin hanci a bakin aikin ba, wannan tasa kungiyar Accountability Lab tare da hadin gwiwar Luminate, gidauniyar Mac Arthur da gidauniyar Ford suka karrama shi da lambar yabo ta ‘Integrity Icon summit award’

Shi dai wannan lambar yabo an kirkire shi ne domin karrama duk wani jami’in gwamnati mai gaskiya, tare da bayyana shi ga duniya don ta san shi domin karfafa ma sauran jami’an gwamnati gwiwa game da yin adalci.

Sauran wadanda aka karrama sun hada da Tani Ali Nimlan, jami’in hukumar kula da ingancin abinci na NAFDAC, Tina Lirmdu, malama a jami’ar Jos, Kacheilon Robert-Ndukwe, malamin sakandari a garin Fatakwal da Christian Ahiauzu, shugaban sashin kimiyya da fasaha a jami’ar Fatakwal.

A jawabinsa, Erhabor yace: “Kiris ya rage na amince da tayin cin hancin da ba don Allah Ya kiyaye ni ba. Wannan labarin daya bayyana ni a yau ha rake karrama ni ya faru ne a lokacin da N800 ne kacal a aljihuna, kuma ni ne kwamandan kare bututun mai a jahar Edo inda na yi kusan shekaru 4.

“Alawus dina na aiki N37,500 ne, kuma ma baya zuwa a lokacin daya kamata, kwatsam sai ga wasu sun min tayin naira miliyan 1.5 somintabi, kuma zasu dinga bani naira miliyan 6 duk sati, a kwana 30 naira miliyan 24 kenan fa!

“Amma saboda rantsuwar dana dauka kafin na shiga aikin Dansanda na cewa ba zan taba karya dokar aiki ba, shi yasa ban amince da wadannan makudan kudade ba, na gwammace na cigaba da amsan N37,500 da basa zuwa a kan lokaci.” Inji shi.

Daga karshe Erhabor yace ya sha suka, an nuna masa tsana da tsangwama, har ma an yi ma rayuwarsa barazana duk don matakin kare mutuncin kansa daya dauka, amma daga karshe gaskiya ta yi halinta, kuma ya samu daukaka a dalilin haka daga ciki da wajen aikinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel