Tsoron kunyar duniya yasa na kashe budurwata bayan na dirka mata ciki – Saurayi

Tsoron kunyar duniya yasa na kashe budurwata bayan na dirka mata ciki – Saurayi

Kira ga jama’a, ya zama wajibi kowa ya dinga rokon Allah Ya shiga tsakaninsa da mugu, a nan wani matashi dan shekara 29 ne ya halaka budurwarsa yar shekara 20 bayan ya dirka mata ciki, inda yace ya yi hakan ne don gudun jin kunyar duniya.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Jigawa ce ta samu nasarar kama matashin mai suna Idris, wanda ya kashe budurwarsa Nafisa Hashimu wai don yana tsoron kallon da za’a masa idan labarin cikin shegen daya dirka mata ya bayyana.

KU KARANTA: Dundum! Boko Haram ta lalata wutar lantarkin garin Maiduguri

Kaakakin rundunar Yansandan, Audu Jinjiri ya bayyana cewa Nafisa Hashimu, wanda bazawara ce ta dade tana soyayya da Idris, don haka ranar da ta bashi labarin tana dauke da cikinsa, ta fada masa ne cikin farin ciki da jin dadi, a zaton ta ta burge.

Sai dai jin wannan labari keda wuya, sai Idris ya harkuza, nan da nan fuskarsa ta canza, ai kuwa sai ya dauki wuka ya caka mata a ciki, inda nan take Nafisa ta fadi matacciya, sa’annan ya dauke gawarta ya kai ta cikin daji wajen garin Daneji, kilomita 22 daga garin Ringim.

A cewar matashin; “Ina jin kunyar yadda jama’a zasu kalle mu bayan ta haifi dan shege, don haka na dauki hukuncin kashe ta da kaina domin na kubuta daga abin kunya.”

Daga karshe Audu Jinjiri yace zasu gurfanar da shi gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike domin ya fuskanci hukuncin daya dace da shi.

Ya kamata iyaye su dage a kan tarbiyyar yaransu, haka nan samari da yan mata su sani idan har ba su da nufin aure, toh basu da uzurin fara soyayya, ta hka ne za'a rage samun ire iren ta'asar nan a tsakanin al'umma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel