Barawo ya diro daga gidan sama mai hawa 2, ya karya wuya a jahar Imo

Barawo ya diro daga gidan sama mai hawa 2, ya karya wuya a jahar Imo

Wani barawo mai suna uche Akunacha mai shekaru 41 ya aikata ma kansa aika aika ta hanyar kashe kansa da kansa a lokacin da ya tafka tsalle daga gidan sama mai hawa biyu don ya tsere daga mutanen da ya yi ma sata.

Jaridar Punch ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Janaru a jahar Imo inda Uche ya shiga dakin wani mutumi Orlando Ikeokwu dake cikin wani bene mai hawa biyu, da nufin tafka masa sata.

KU KARANTA: Mai rangwamen hankali ya jika makwabcinsa da fetur, ya banka masa wuta

Sai dai ya yi rashin sa’a mai kayan ya kama shi, inda ya kwantsama ihu, amma sai Uche barawo ya fita a guje yana neman yadda zai tsira da ‘na bakin sa’, ganin haka ta sa ya yanke shawarar dirowa daga gidan saman, ashe tafiyar kenan, sai ya dira ta wuya, kai tsaye ya zarce barzahu.

Kaakakin Yansandan jahar yace: “Tochukwu Okafor dake titin kwaleji a Mgbidi ne ya kai rahoton cewa ya koma gida sai ya tarar an lalata masa kofar dakinsa, shigar sa ciki ke da wuya sai ya tarar da wani mutumi dauke da Spanner yana bincike masa daki.

“Nan ta ke ya daka ma mutumin wawa tare da kwantsama ihun neman agaji, amma mutumin ya kufce, kuma ta daka tsalle daga gidan sama mai hawa biyu, inda ya fadi ta kai. Nan da aka garzaya da shi asibiti, kuma a gaban matarsa ya amsa laifinsa, amma ya mutu bayan wani dan lokaci.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel