An yi arangama tsakanin yan Shia da jami’an Yansanda a babban birnin tarayya Abuja

An yi arangama tsakanin yan Shia da jami’an Yansanda a babban birnin tarayya Abuja

Akalla mabiyan darikar Shia 5 na kungiyar yan uwa Musulmai, watau Islamic Movement in Nigeria, IMN, ne suka samu munanan rauni a sakamakon wata arangama da suka yi da jami’an rundunar Yansandan Najeriya a Abuja.

Jarida The Nation ta ruwaito an yi wannan dauki ba dadi ne yayin da yan shian suke gudanar da muzahara a daidai shataletalen Berger dake cikin babban birnin tarayya Abuja, inda Yansanda suka cimmasu.

KU KARANTA: Gwamnatin Kaduna ta garkame bankuna guda 3 saboda kin biyan haraji

Yan shian sun zanga zangar ne da nufin tilasta ma gwamnatin Najeriya sakin jagoran su, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da matarsa Zeenatu, dake daure a wani gidan gyaran halayya a jahar Kaduna.

Wani dan Shia ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa: “A yanzu da nake maka magana yansanda sun kashe mana mutane biyar.”

Idan za’a tuna gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin jahar Kaduna ba za ta taba sakin El-Zakzaky ba har sai babbar kotun jahar Kaduna ta yanke hukunci a karar da suka shigar da shi.0

El-Rufai ya bayyana haka ne a makon da ta gabata yayin da yake tattaunawar kai tsaye da al’ummar jahar Kaduna, inda yake amsa tambayar da aka yi masa game da halin da Zakzaky yake ciki.

A cewar gwamnan, duk ihun masu ihu, duk zanga zangar masu zanga zanga ba zai sa ya saki Zakzaky ba, har sai kotu ta yanke masa hukunci, sa’annan ya yi alkawari zai dabbaka duk hukuncin da kotu ta yanke.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel