Ma'aikatar Bogi: Za a Gurfanar da Adeyemi gaban Kotu, Na Kusa da Tinubu Zai Bada Shaida

Ma'aikatar Bogi: Za a Gurfanar da Adeyemi gaban Kotu, Na Kusa da Tinubu Zai Bada Shaida

  • Rundunar 'yan sandan Najeriya za ta gurfanar da Adeniyi Adeyemi a gaban kotu kan zarge-zargen da suka shafi kafa hukumar PFIC
  • Ana zargin Adeniyi Adeyemi da jagorantar wata hukuma mai suna PFIPC wadda gwamnati ta ce ba ta san da zamanta ba
  • Manyan jami'an gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da wasu mutane ake sa ran za su ba da shaida a shari'ar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Rundunar 'yan sandan Najeriya za ta gurfanar da Adeniyi Adeyemi, wanda ke ikirarin shi ne shugaban wata hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC).

Rundunar 'yan sandan za ta gurfanar da Adeniyi Adeyemi a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Talata, 14 ga watan Yulin 2026.

Yan sanda za su gurfanar da Adeniyi Adeyemi
Adeniyi Adeyemi zaune a cikin ofis Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta kawo rahoton cewa a a gurfanar da Adeyemi a gaban Mai shari'a Mohammed Umar na babbar kotun tarayya.

Kara karanta wannan

Sarkin Zazzau ya ba da shawara kan gudanar da sahihin zabe a Najeriya

Wadanne tuhume-tuhume ake yi wa Adeyemi?

'Yan sanda sun gurfanar da Adeyemi tare da wasu mutum biyu bisa tuhume-tuhume takwas da suka hada da zargin yin takardun bogi da yin sojan gona a shari'ar mai lamba FHC/ABJ/CR/562/2025.

Mai gabatar da kara na rundunar 'yan sanda, Wisdom Madaki, ya shigar da karar ne a ranar 27 ga Nuwamba, 2025.

A ranar 16 ga Yunin 2026, an kasa ci gaba da shari'ar da aka tsara domin gurfanar da Adeyemi saboda bai halarci kotu ba, inda aka bayyana cewa yana fama da rashin lafiya.

Manyan jami'ai za su ba da shaida

Takardun kotu sun nuna cewa daga cikin shaidun da masu gabatar da kara ke shirin gabatarwa akwai shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.

Sauran sun hada da Paul Emmanuel, Jeremiah Imoukhede da Ituah Sylvester, jaridar TheCable ta kawo rahoton.

Haka kuma akwai ma'aikatan Ofishin Akanta Janar na Tarayya, Akimbo Shola, da Adamu Balongu, mataimakin sufeton 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke 'yar kasar waje mai safarar miyagun kwayoyi ga 'yan ta'adda

Karin shaidun da ake sa ran za su bayyana

Sauran shaidun sun hada da Ojo Victor, Omeh Amarachukwu da Wakili Saidu, wadanda ake zargin an tura su aiki tare da Adeyemi a hukumar da ake cewa ba a san da zaman ta ba.

Haka kuma Joy Ngwoke, mai otal din Kachi Hotel da ke Abuja, da Ven Okoriko, faston cocin St. Matthew's Anglican Church da ke Maitama, suna cikin jerin shaidun.

'Yan sanda za su gurfanar da Adeniyi Adeyemi
Shugaban ma'aikatar bogi, Adeniyi Adeyemi Hoto: Adeniyi Adeyemi Matthew
Source: Facebook

Takardun da masu gabatar da kara za su gabatar

Masu gabatar da kara sun ce za su gabatar da rahoton binciken 'yan sanda, koken da Femi Gbajabiamila ya rubuta mai kwanan wata 17 ga Oktoba, 2025, da kuma takardar nadin mukamin shugaban kasa da ake zargin ta bogi ce mai kwanan wata 8 ga Maris, 2024.

Sauran takardun sun hada da bukatar neman amincewa da Adeyemi ya aika wa ma'aikatar harkokin waje, takardun amincewar bude asusu a CBN, bukatar ba hukumar damar gudanar da harkokinta da kanta da ya aika wa Ofishin Akanta Janar na Tarayya, da kuma takardar amincewar fara aikin PFIPC.

Kara karanta wannan

Sojoji sun samu gagarumar nasara bayan kashe manyan yan ta'adda 8 a Katsina

Har ila yau, akwai wasikar neman hadin gwiwa da ma'aikatar wajen mallakar filaye da bude ofisoshi a dukkan jihohi 36 na tarayya, bayanan shaidu, bayanan wadanda ake tuhuma da kuma hotuna.

Adeyemi ya yaudari Benjamin Kalu

A wani labarin kuma, mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ya bayyana cewa Adeniyi Adeyemi, wanda ya yi ikirarin shi ne shugaban hukumar PFIPC, ya yaudare shi.

Benjamin Kalu ya ce ya karbi bakuncin Adeyemi ne bayan ya samu wata wasiƙa da ta yi kama da ta hukuma daga fadar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng