2026: Lamine Yamal Ya Fadi Kasar da Za Ta iya Doke Faransa a Gasar Kofin Duniya
- Lamine Yamal ya ce Spain da Faransa su ne ƙasashe biyu mafi ƙarfi a gasar Kofin Duniya, amma ya ce kasarsa na da ƙarfin doke Faransa
- Spain ta kai wasan dab da na ƙarshe bayan ta doke Belgium, inda Mikel Merino ya ci ƙwallar nasara duk da ƙoƙarin abokan hamayyarsu
- Wanda ya yi nasara tsakanin Spain da Faransa zai kai wasan ƙarshe, inda zai fafata da wadda ta tsallake daga ɗaya wasan dab da na karshen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Ɗan wasan gefe na Barcelona da tawagar ƙasar Spain, Lamine Yamal, ya bayyana cewa Spain da Faransa su ne ƙasashe biyu mafi ƙarfi a gasar cin Kofin Duniya ta FIFA da ake yi a halin yanzu.
Yamal ya kuma nuna cikakken ƙwarin gwiwa cewa tawagar La Roja za ta iya doke Faransa a wasan dab da na ƙarshe da za a buga ranar Talata.

Source: Getty Images
"Ba mu jin tsoron Faransa" - Yamal
Yamal ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da aka gudanar kafin wasan, kamar yadda rahoton New York Times ya nuna.
A cewarsa, mutane da dama sun daɗe suna fatan ganin wannan karawa tsakanin manyan ƙasashen biyu.
"Tun bayan fara gasar, mutane da yawa suna jiran wannan wasa. A gare ni, Spain da Faransa su ne ƙasashe biyu mafi ƙarfi a wannan Kofin Duniya."
Ya ƙara da cewa:
"Ba mu jin tsoron Faransa. Idan akwai ƙasar da za ta iya doke Faransa, to ita ce Spain."
Spain ta nuna ƙwarewa a gasar
Spain ta kasance cikin ƙasashen da suka fi jan hankali a gasar, bayan ta kai wasan dab da na ƙarshe sakamakon doke Belgium da ci 2-1 a wasan daf da na kusa da na ƙarshe.
A wannan wasa, Spain ta mamaye wasan ta fuskar riƙe ƙwallo da ƙirƙirar damammaki, duk da cewa Belgium ta nuna ƙwazo musamman a tsakiya duk da rashin wasu fitattun 'yan wasanta.
Belgium ta rama ƙwallon da Spain ta fara ci ta hannun Charles De Ketelaere, bayan kyakkyawan haɗin gwiwa tsakanin Kevin De Bruyne da Timothy Castagne.
Wannan ne karo na farko da aka zura wa Spain ƙwallo bayan mintuna 649 ba tare da an ci ta ba, wanda ya zama ɗaya daga cikin mafi tsawon tarihin gasar cin Kofin Duniya.

Source: Getty Images
Wasan da duniya ke jira
Rahoton da BBC ta fitar ya nuna cewa Spain da Faransa na daga cikin ƙasashen da aka fi bai wa damar lashe gasar tun kafin a fara ta.
Spain na neman lashe Kofin Duniya karo na biyu bayan nasararta ta shekarar 2010, yayin da Faransa ke neman ɗaukar kofin karo na uku bayan nasarorin da ta samu a 1998 da 2018.
Wanda ya yi nasara a wasan na ranar Talata zai tsallake zuwa wasan ƙarshe, inda zai kara da wadda ta yi nasara a ɗaya wasan dab da na ƙarshe.
Yamal ya tsokano Isra'ila
A wani labari, mun ruwaito cewa, kasar Isra’ila ta yi martani mai zafi ganin ɗan wasan Barcelona ya daga tutar Falasdinu yayin murnar lashe gasar La-liga.
Abin da tauraron kulob din Barcelona ya yi ya jawo maganganunm yayin da wasu yabonsa duk da suka da ya ke sha a duniya.
Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce matakin dan wasan ya tayar da kiyayya, yayin da ake ci gaba da rikicin Gaza tsakanin Isra’ila da Hamas.
Asali: Legit.ng


