Asiri ya tonu: 'Yan sanda na sayarwa da matsafa masu laifi kan kudi N80,000

Asiri ya tonu: 'Yan sanda na sayarwa da matsafa masu laifi kan kudi N80,000

- A ranar Talata ne kwamishinan 'yan sandan jihar Kwara ya bayyana cewa an sauya wa wasu 'yan sanda wajen aiki

- Ado Lawan ya ce hakan ya biyo bayan zarginsu da ake yi da siyar da masu laifi ga matsafa a kan naira dubu tamanin

- Ya ce duk da ba a tabbatar da zargin ba, an sauya musu wuraren aikin ne saboda gudun barkewar rigima a yankuna

A jiya Talata ne kwamishinan 'yan sandan jihar Kwara, Lawan Ado ya ce an sauyawa wasu 'yan sanda wajen aiki saboda zargin da ake musu.

Ado ya ce mazauna yankin sun zargi 'yan sandan da laifin siyar da wadanda ake zargi masu laifi ne ga matsafa a kan naira dubu tamanin kacal, kamar yadda Jaridar Al'ummata ta wallafa.

Kwamishinan ya sanar da hakan ne a ziyarar da ya kaiwa gwamnan Rotary International, Mbanefo Nnika tare da rundunar 'yan sandan na jihar.

Kwamishinan ya ce, duk da zargin karya ne, ya sauya musu wajen aikin domin gujewa rikici. Ya kara da cewa babu wanda ya taba kai korafin nan ballantana shaida cewa 'yan sandan na siyar da masu laifi ga matsafa.

KU KARANTA: An yiwa Lakcara korar kare bayan ya nemi lalata da dalibar shi

Kamar yadda ya ce, "amma mun sauyawa 'yan sandan wurin aiki. Sama da rabinsu an canza musu wajen aiki inda sauran kuma ana kan shirin canza musu".

Nonka ya bayyana cewa kungiyar Rotary Club ta kashe dala biliyan 7.3 a fadin duniya sannan ta kashe naira miliyan 300 a Najeriya don yakar Polio.

Ya yi kira ga iyaye da su yi kokarin kai yaransu wajen riga kafin cutar Polio don abin tausayi ne a ce akwai iyayen da basu so a yi wa yaransu allurar riga kafin a Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel