Magidanci Ya Hau Matarsa da Duka kan Abinci, Allah Yayi Mata Rasuwa a Nasarawa

Magidanci Ya Hau Matarsa da Duka kan Abinci, Allah Yayi Mata Rasuwa a Nasarawa

  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da kama wani mutum bisa zargin dukan matarsa har ta mutu a jihar Nasarawa
  • Rahotanni sun nuna cewa magidancin da ake zargi da aikata wannan danyen aiki, ya ce ya daki matar ne saboda ta ƙi dafa masa abinci
  • Kwamishinan 'yan sanda na jihar Nasarawa ya ba da umarnin mika lamarin zuwa ssshen SCID domin gudanar da cikakken bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa - Rundunar 'Yan Sandan Jihar Nasarawa ta kama wani mutum mai suna Musbawu Amodu mai shekaru 30 bisa zargin dukan matarsa mai shekaru 20 har ta mutu.

Kara karanta wannan

Matashi mai shekaru 23 ya hallaka Farfesa da kaninsa cikin wani irin yanayi

Magidancin ya hau matarsa da duka ne har ta rasa ranta bayan wata takaddama da ta barke a tsakaninsu a Angwan Yahaya, Agyaragu, karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa.

Yan sanda
Jami'an hukumar yan sanda ta Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Miji ya kashe matarsa a Nasarawa

'Yan sanda sun ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi, inda aka kai rahoto ofishin 'yan sanda na Agyaragu da misalin karfe 12:30, kamar yadda tashar Channels tv ta kawo.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, SP Ramhan Nansel, ya ce jami'an 'yan sanda sun garzaya wurin da abin ya faru, sannan aka kai gawar marigayiyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami'ar Tarayya da ke Lafia domin gudanar da bincike.

A cewar 'yan sanda, an kama Musbawu Amodu, kuma yayin da ake yi masa tambayoyi ya amsa cewa ya fara bugun matrsa ne cikin fushi bayan ta ki dafa masa abinci.

Rundunar ta ce sabanin da ya fara tsakanin ma'auratan ya rikide zuwa fada, wanda daga bisani ya yi sanadin mutuwar matar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke 'yar kasar waje mai safarar miyagun kwayoyi ga 'yan ta'adda

'Yan sanda sun fara gudanar da bincike

Rahotanni sun nuna cewa wanda ake zargin ya nuna nadama kan abin da ya faru har ya kashe matarsa juma uwar yaransa.

Tribune Nigeria ta ruwaito cewa marigayiyar ta rasu ta bar yara biyu, namiji da mace, bayan shafe shekara shida da aurensu.

Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Nasarawa, Shetima Mohammed, ya ba da umarnin a mika lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) da ke Lafia domin gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa.

Ya tabbatar wa al'ummar jihar cewa za a yi adalci, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Nasarawa.
Taswirar jihar Nasarawa da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kwamishina ya yi Allah wadai da kisan

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Jiragen sojoji sun far wa taron 'yan bindiga 300 a jihar Zamfara

Kwamishinan ya yi tir da duk wani nau'in tashin hankali a cikin gida, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma wanda za a iya kauce masa.

Ya bukaci ma'aurata su rika warware sabanin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da bin doka, maimakon amfani da tashin hankali.

Matar aure ta soka wa mijinta wuƙa

Kun ji cewa wata matar aure yar kimanin shekara 23, Sadiya Lawal ta yi yunkurin kashe mijinta ta hanyar yanka masa wuya yana cikin barci a jihar Katsina.

Mutumin, mai suna Jamilu Ibrahim, ya tsira daga harin kuma yana samun kulawa a asibiti, yayin da dakarun yan sanda suka cafke matarsa.

Rundunar ta ce matar na tsare a hannunta yayin da ake ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da ita a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262