Farashin Fetur Zai Lula, Dangote Zai Cigaba da Saida Mai da Dizal a Dala
- Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur, dizal, da man jirgi da Naira, ta maida cinikayya da dalar kasar Amurka
- Wannan mataki ya biyo bayan matsin lambar da aka samu a tsarin da ake kai da Gwamnatin Tarayya a baya
- Masana da masu ruwa da tsaki na fargabar wannan sauyi zai kara tsadar man da sauran kayayyakin mai ga talakawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Ana tsoron akwai yiwuwar tashin farashin mai a sakamakon matatar Dangote za ta fara saida duka kaya da Dalar Amurka.
Idan aka koma ciniki da Dala maimakon Naira, wannan zai jefa kudin Najeriyan a matsala kuma ya jawo mai ya kara tsada a gidaje.

Source: Getty Images
Dangote: Saida mai da Dala zai tashi farashi
Wani rahoto daga Daily Trust ya nuna cewa rikicin da ake fama da shi a gabas ta tsakiya ya sa farashin danyen mai ya tashi.
Wadannan canji za su yi tasiri a nan Najeriya, a ga sauyin kudin litar fetur da dizil saboda kokarin neman kudin waje zai karu.
dMasana harkar mai sun ce idan babban matatar Afrikar ta koma ciniki da Dala, dole mai ya kara kudi kuma kaya su kara tsada.
Ban da zancen farashi, wata matsala da rikicin Iran da Amurka da Israila za ta iya haifarwa ita ce raguwar mai a kasuwannin duniya.
Me ya jawo Dangote zai koma cinikin Dala?
Majiya daga kamfanin NNPLC ta ce ana samun matsala a cinikin da matatar Dangote ta ke yi da Najeriya da kudin gida.
An kawo tsarin ne da nufin matatar ta saye danyen man Najeriya a Naira, wannan zai saukake mata shiga kasuwannin duniya.
A gefe guda, Najeriya za ta amfana da saukin farashin kayan mai da karin darajar Naira saboda an rage rububin Dala a kasuwa.
Labarin da tashar Arise ta fitar ya nuna Gwamnatin Najeriya ba ta iya sama wa Dangote isasshen danyen man da yake bukata.

Source: Getty Images
Tunda dole matatar Dangote ta shiga kasuwannin duniya, rahoton ya ce wajibinsu ne su ma su yi lissafi da Dala ba a Naira ba.
Wani da ya yi magana a asirce, ya bayyana cewa matatar tana fuskantar barazana saboda sayen danyen mai da ta ke yi a Dala.
Masana sun yi karin haske cewa neman dala da ‘yan kasuwa za su rika yi domin sayo mai zai kara fito da raunin Naira a kasuwa.
Bugu da kari, watakila abin da ake sayen kowane lita na fetur da dizil a gidajen mai zai canza kwanan nan duk da kukan da ake yi.
Mutane za su yi kudi da kamfanin Dangote
Labari ya zo cewa an sa ladar N500, 000 idan aka tona asirin direbobin Dangote da ke daukar mutane da kaya ba bisa ka'idar aiki ba.
Dangote Industries Limited (DIL) ya bukaci jama'a da su kai karar duk wani direba da aka samu ya dauki mutane ko kaya domin ya samu kudi.
Sanarwa ta zo cewa an ɗauki matakin ne domin kare kayayyakin kamfanin da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkar zirga-zirga.
Asali: Legit.ng

