Lamari ya ta’azzara: Yan bindiga kai ma jami’an Yansanda farmaki, sun dauke makamansu

Lamari ya ta’azzara: Yan bindiga kai ma jami’an Yansanda farmaki, sun dauke makamansu

Wasu gungun yan bindiga dadi sun kai ma jami’an rundunar Yansandan Najeriya hari a jahar Delta a yayin da suke aikin binciken motoci a shingen binciken ababen hawa dake cikin garin Asaba, babban birnin jahar Delta.

Jaridar Punch ta ruwaito lamarin ya auku ne da misalin karfe 9 na dare a kasuwar Abraka dake cikin garin Asaba, inda yan bindigan suka jikkata Yansanda guda uku, sa’annan suka kwashe bindigoginsu guda uku.

KU KARANTA: Mai rangwamen hankali ya jika makwabcinsa da fetur, ya banka masa wuta

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yanzu haka Yansanda sun can a cikin mawuyacin hali a wani asibiti da ba’a bayyana sunansa ba suna samun kulawa. Wasu ganau ba jiyau ba sun tabbatar da cewa yan bindigan sun yi amfani da adda wajen kakkafta ma Yansandan sara.

“Bayan sun sun kai musu harin, miyagun sun cigaba da tafiya a kan titi, kafin daga bisani suka bace bat!” inji shaidan gani da ido wandsa ya kara da cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da Yansanda suka ajiye makamansu suna amsan cin hanci daga direbobin keke napep.

Sai dai kwamishinan Yansandan jahar, Hafiz Inuwa ya tabbatar da aukuwar harin, amma yace a iya saninsa bindigu biyu miyagun suka kwashe ba bindigu uku ba. “Na samu labarin cewa ba wannan bane karo na farko da ake samun irin wannan harin.

“Amma dai wannan ne karo na farko da aka kaddamar da irin wannan harin tun bayan zuwana jahar nan a matsayin kwamishinan Yansanda, amma da ikon Allah da kuma jajircewarmu hakan ba zai kara faruwa ba.

“Cikin kwanaki 8 da na zuwa na, na kwace makamai guda 10 da miyagu suke amfani dasu wajen aikata munanan ayyuka a jahar, muna cigaba da bin sawunsu, kuma duk wanda muka kama zai ji a jikinsa.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng