An yi ba’a yi ba: Barawo ya sulale daga Kotu a lokacin da Dansanda yake sharbar barci

An yi ba’a yi ba: Barawo ya sulale daga Kotu a lokacin da Dansanda yake sharbar barci

Zakara ya baiwa wani matashi dan shekara 20 da ake tuhuma da tafka laifin sata mai suna Hassan Sulaiman sa’a yayin da ya tsere daga hannun Dansanda a jahar Legas a daidai lokacin da ake shirin gurfanar da shi gaban kotu.

Daily Trust ta ruwaito matashin ya sulale ne a harabar kotu bayan an dauko shi tun daga ofishin Yansanda dake Iponri Surulere, zuwa wata babbar kotun majistri bisa tuhumar da ake masa na sata.

KU KARANTA: Turi ya kai bango: Mutanen gari sun yi fito na fito da yan bindiga, sun kashe 5 a Filato

Sai dai ko da aka isa kotun, sai jami’in dansandan da zai gabatar da tuhume tuhumen da rundunar Yansanda take dasu a kan say a bige da barci, har ma da sharbar minshari, ganin haka matashin yace “kafa mai na ci ban ba ki ba”, daga nan ya ranta ana kare.

Yansanda na tuhumar Hassan Sulaiman ne da kutsawa cikin wani gida mai lamba 96 titin Brickfield a unguwar Ebutte-Meta a ranar 16 ga watan Janairu tare da satar injin famfon tuka tuka da kudinsa ya kai N65,000, na’aurara Janareta N35,000 da murhun girki da kudinsa ya kai N5,000.

Sai dai tuni rundunar Yansandan jahar Legas ta shiga farautar matashin, inda ta sanar da tserewarsa tare da kira ga jama’a dasu gaggauta sanar da ofishin Yansanda mafi kusa idan sun yi ido hudu da shi.

A wani labarin kuma, Yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun kai wani mummunan samame a unguwar Abebe dake cikin karamar hukumar Keana na jahar Nassarawa, inda suka kashe mutane hudu babu laifin fari balle na baki.

Baya ga kashe mutane hudu, makaharan sun raunata wasu mutane biyu sakamakon harbin bindiga. Wani daga cikin wadanda suka tsallake harin, Vitalis Adam ya bayyana wadanda suka mutu kamar haka.

“Wani jami’in Cocin St Augustine, Augustine Avertse da mahaifinsa Avertse Akaa’am, Uwongul John Akodi da kuma wani mutumi mai suna Monday, yan bindigan sun harbe su ne yayin da suke kokarin tserewa cikin daji.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel