An karrama jami'in dan sanda da ya ki karbar cin hancin N6m (Hotuna)

An karrama jami'in dan sanda da ya ki karbar cin hancin N6m (Hotuna)

- Nagarta bata taba zubar da mutunci ga kowa ba ko kuma tozarta dan Adam ba

- An karrama wani dan sanda mai suna Francis Erhabor a Akwa Ibom da kambun nagartar shekarar 2019

- Sunan Erhabor ya daukaka ne bayan da ya ki karbar cin hancin naira miliyan 6 don ya bari a saci man fetur a Edo

Babu shakka nagarta abin jinjinawa ce. Duk da dai akwai matukar wahala zama mai nagarta a yayin da rashawa ta yi katutu a wuri. Wannan kuwa shi ne labarain wani dan sanda a karamar hukumar Ita da ke jihar Akwa Ibom mai suna Francis Erhabor. Dan sandan ya ki karbar cin hancin naira miliyan 6 ne saboda kada ya gurbata tsaron da ke yankin.

An karrama jami'in dan sanda da ya ki karbar cin hancin N6m
An karrama jami'in dan sanda da ya ki karbar cin hancin N6m
Asali: Twitter

A ranar Talata, 21 ga watan Janairu kuwa aka yi wa Erhabor karramawar ba zata da kambun girmamawa saboda nagartarsa daga Accountability Lab, Luminate, MacArthur and Ford Foundation a Abuja.

DUBA WANNAN: 2023: Dattijan 'yan siyasar arewa 4 da suka cancanci samun mulkin shugaban kasa

Dan sandan ya ce an yi masa alkwarin naira miliyan 6 a kowanne mako matukar zai kawar da idonsa daga wannan bututun man da ke jihar Edo. Amma kuma sai nagartaccen jami'in ya ce baya bukata duk da kuwa N37,500 ya ke karba a matsayin alawus dinsa na kowanne wata.

An karrama jami'in dan sanda da ya ki karbar cin hancin N6m
An karrama jami'in dan sanda da ya ki karbar cin hancin N6m
Asali: Twitter

Ya ce ya jajirce ne tare da kawar da kai a kan wadannan makuden kudin ne saboda rantsuwarsa ta farko da ya yi yayin shiga aikin ya ke girmamawa. Dan sandan ya bayyyan irin tsoratawa tare da barzanar da ya dinga samun bayan ya ki amincewa da cin hancin.

Erhabor ya ce ya yi wa Ubangiji alkawarin cewa babu abinda zai girgiza shi kuma ya roki kariya daga cin haram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel