Trump Ya Daina Boye Boye, Ya Fadi abin da Zai Faru idan Amurka Ta Kwace Hormuz

Trump Ya Daina Boye Boye, Ya Fadi abin da Zai Faru idan Amurka Ta Kwace Hormuz

  • Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta kula da mashigar ruwan Hormuz tare da neman a biya ta kuɗin tsaro da za ta ba jirage
  • Trump ya zargi Iran da karya yarjejeniyar da aka cimma kan sake buɗe mashigar, lamarin da ya jawo sake musayar hare-hare
  • Sai dai kuma, ita Iran ta ce ba za ta buɗe mashigar Hormuz ba har sai Amurka ta dakatar da ayyukan sojinta, yayin da rikicin ke kamari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ƙasarsa na shirin karɓar alhakin kula da mashigar Hormuz, yana mai cewa ya kamata ƙasashen da ke cin moriyar tsaron hanyar su biya Amurka kuɗin wannan aiki.

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira ta wayar tarho da tashar Fox News, yayin da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ke ci gaba da ƙamari.

Kara karanta wannan

Rashin sani: Shaguben da sanatan Amurka ya yi ga Iran kwana 5 kafin ya mutu

Trump ya ce Amurka za ta sanya haraji ga jiragen da za ta rika ba kariya a mashigar Hormuz
Shugaban Amurka, Donald Trump da mashigar ruwan Hormuz. Hoto: Getty Images
Source: UGC

"Za mu kare mashigar kuma za a biya mu"

A cewar Trump, Amurka za ta kasance mai kula da mashigar, wadda ke daga cikin muhimman hanyoyin jigilar ɗanyen mai da iskar gas a duniya, in ji rahoton USA Today.

Ya ce:

"Za mu riƙe mashigar, kuma mai yiwuwa mu kasance masu tafiyar da ita. Za mu zama masu kula da mashigar. Wataƙila ma mu kira kanmu 'masu tsaron mashigar'. Kuma ya kamata a biya mu saboda wannan."

Trump ya ƙara da cewa ba zai dace Amurka ta ci gaba da kashe kuɗaɗe wajen kare hanyar ba tare da samun wani sakamako ba.

Ya ce ƙasashen da ke amfana da tsaron mashigar suna da ƙarfin tattalin arziki, don haka ya kamata su biya kuɗin aikin da Amurka za ta yi.

Trump ya zargi Iran da karya yarjejeniya

Aljazeera ta rahoto cewa shugaban Amurka ya kuma zargi Iran da karya yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙasashen biyu kan sake buɗe mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Yadda Moroko da ƙasashen Afirka 9 suka taka leda a gasar Kofin Duniya ta 2026

A cewarsa:

"Mun cimma yarjejeniya, komai ya kammala, amma daga baya suka karya ta. Kullum haka suke yi. Mun yi yarjejeniyoyi da su har sau 10, don haka za mu ɗauki mataki mai tsauri a kansu."
Sojojin Iran sun ce ba za su bude mashigar Hormuz ba har sai idan Amurka ta janye sojojinta.
Wasu daga cikin sojojin Iran suna atisaye. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta gindaya sharadi kan buɗe Hormuz

A nata ɓangaren, dakarun IRGC na Iran sun ce hanyar da za a bi wajen dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz ita ce Amurka ta dakatar da ayyukan sojinta a yankin.

Rundunar ta yi gargaɗin cewa ci gaba da abin da ta kira katsalandan daga Amurka na iya haifar da ƙarin rikice-rikice da za su shafi kasuwannin mai da iskar gas a duniya.

Iran ta ce ta kai hare-hare kan wasu sansanonin sojin Amurka da ke yankin Tekun Fasha, yayin da ta ci gaba da rufe mashigar Hormuz.

Kasar Iran ta kai hare-hare Amurka

A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar sojojin Iran ta IRGC ta yi ikirarin cewa ta kai wani "mummunan hari kuma na ba-zata" kan wuraren da Amurka ke amfani da su a Oman.

Kara karanta wannan

Tinubu ya watsawa majalisa ƙasa a ido, ya ƙi sanya hannu kan sababbin kudurori 2

IRGC ta yi ikirarin kai hari kan wuraren tallafin kayan aiki da wuraren loda man fetur da jiragen ruwan yakin Amurka masu daukar jiragen sama ke amfani da su a tashar jiragen ruwa ta Duqm.

Rundunar ta yi ikirarin cewa ta lalata cibiyar bada umarni da sarrafawa tare da wurin da ake ajiye jiragen yaki marasa matuka na MQ-9 a sansanin Prince Hassan Air Base.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com