Taron Tuna Buhari: Tinubu, Gowon, Shettima, Zulum da Sauransu Sun Magantu
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa tasirin marigayi Muhammadu Buhari na ci gaba da bayyana a Najeriya bayan shekara guda da rasuwarsa
- Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya wakilci Tinubu a taron addu'ar tunawa da Buhari da aka yi Abuja ranar Litinin
- An sanar da kafa wata gidauniya don kiyaye tarihin tsohon shugaban kasar, yayin da Yakubu Gowon da sauran manyan mutane suka halarci taron
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce abubuwan da marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi na ci gaba da amfanar Najeriya.
Bola Tinubu ya bayyana cewa canji da Buhari ya yi daga shugabancin soja zuwa dimokiradiyya ya sa shi ya zama mutumin da ba kasafai ba a tarihin kasar.

Source: Facebook
Shettima ya wallafa a Facebook cewa Tinubu ya gabatar da wannan jawabi ne ta bakinsa, a wani taro da aka yi ranar Litinin a Abuja don addu'a da tunawa da Buhari bayan shekara daya da rasuwa.
Kiran Tinubu ga shugabanni
Shugaba Tinubu ya roki shugabannin siyasa da jami'an gwamnati da su bi sawun Buhari wajen kiyaye gaskiya, saukin kai da kuma ladabi ga kasa.
Tinubu ya tuna alakar da suke da ita da Buhari a fagen siyasa, yana mai kwatanta shi da abokin tafiya a doguwar hanyar ci gaban kasar.
Ya kara da cewa duk da duk matsin lamba da ce-ce-ku-ce da suke tattare da mulki, Buhari ya samu goyon bayan talakawan Najeriya har ya sauka daga mulki.
Ya ce amincewa irin wannan ita ce daya daga cikin tarihin da shugaba zai iya bari a baya, wanda ba ya zuwa a banza sai an samu ta hanyar tsawon lokaci ana nuna gaskiya da rikon amana.
Shugaban kasa ya kuma tabbatar matar tsohon shugaban kasa, Aisha Buhari, da dukkan iyalan shi, cewa gwamnatin tarayya da mutanen Najeriya za su kasance a tare da su a kowane lokaci.

Source: Facebook
Za a kafa gidauniyar Buhari
A taron, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya sanar da cewa iyalai da abokan Buhari sun yanke shawarar kafa wata gidauniya don kiyaye tarihinsa.
Ya ce dukkan shugabannin bangarori daban-daban da kuma talakawan Najeriya suna da alhakin kiyaye tarihin Buhari da koyi da kyawawan halayensa.
Tsohon shugaban kasa, Yakubu Gowon ya tuna abubuwan da suka shafi rasuwar Buhari, yana mai cewa yadda mutane suka taru ya nuna ƙaunar da aka yi masa a ciki da wajen Najeriya.
Hadimin Shettima, Stanley Nkwocha ya wallafa a Facebook cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ce taron zai ba da damar nazari kan rayuwar shugaban da ayyukansa.
Aisha ta yaba wa Buhari
A wani labarin, mun kawo muku cewa matar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta yaba wa marigayin kan abubuwan da ya yi.
Yayin wani taro a Katsina, Aisha Buhari ta ce marigayin ya bayar da gudunmuwa sosai wajen inganta ilimi a lokacin mulkinsa.
Yayin da ta ke magana a kan tarihin da ya bari, matar tsohon shugaban kasar ta ce za a dauki tsawon lokaci ana tunawa da Muhammadu Buhari.
Asali: Legit.ng

