Manyan Labarai A Yau
Hukumar shari'a ta kasa (NJC) ta samu korafe-korafe kan wasu alkalai. Hukumar NJC ta kuma ba da shawarar nada sababbin alkalai a kotun daukaka kara.
Tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama, ya tuna baya kan yarjejeniyar da ya kulla da kasar Iran. Ya ce an cimma yarjejeniyar ba tare da kashe kowa ba.
Mayakan Hezbollah sun kai hare-hare kan sojojin Isra'ila da ke Kudancin Lebanom. Harin ya yi sanadiyyar hallaka wani sojan Isra'ila mai shekara 20.
Babban jigo a jam'iyyar hadaka ta ADC, Kenneth Okonkwo ya yi kalamai masu kaushi kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi saboda komawa NDC..
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya yi garambawul a gwamnatinsa. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya sauyawa wasu kwamishinoni wuraren aiki.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da sako ga mambobin jam'iyyar APC kan zaben fitar da gwani. Shugaba Bola Tinubu ya bukaci su hada kawunansu.
Dan Majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Abuja Municipal/Bwari, Hon. Obika ya bayyana cewa ya canza jam'iyya ne saboda cika buri da manufofinsa na siyasa.
Tsohon Ministan sufuri kuma mai neman takarar shugaban kasa a karkashin inuwar ADC, Rotimi Amaechi, ya sha alwashin gyara Najeriya cikin shekara hudu.
Tsohon gwamnan jihar Ondo, Olusegun Mimiko, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya. Olusegun Mimiko ya nuna goyon bayansa ga Bola Tinubu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari