Matashin Sojan Israila Ya Bakunci Lahira bayan Harin Mayakan Hezbollah

Matashin Sojan Israila Ya Bakunci Lahira bayan Harin Mayakan Hezbollah

  • Mayakan kungiyar Hezbollah sun harba makamai kan rukunin sojojin Isra'ila da ke a Kudancin kasar Lebanon
  • Daya daga cikin makamin ya fashe a kusa da wani sojan Isra'ila, wanda ya bar duniya duk da kokarin ceto shi da aka yi
  • Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana cewa sojan ya mutu ne yayin fafatawa a Kudancin Lebanon inda ake ci gaba da musayar hare-hare duk da yarjejeniyar tsagaita wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tel-Aviv, Isra'ila - Rundunar sojojin Isra’ila (IDF) ta sanar da cewa mayakan Hezbollah sun hallaka daya daga cikin sojojinta Lebanon.

Rundunar IDF ta bayyana cewa Staff-Sgt. Negev Dagan, ɗan shekara 20 daga Dekel, ya mutu lokacin fafatawa a Kudancin Lebanon.

Mayakan Hezbollah sun kashe sojan Israila
Wasu sojojin Isra'ila a bakin daga Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar IDF ta sanya a shafinta na X a ranar Juma'a 15 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Yadda harin sojojin sama ya hallaka farar hula da 'yan ta'adda a Zamfara

Sojan Isra'ila ya mutu a Lebanon

Negev Dagan ya ji rauni ne lokacin da mayakan Hezbollah suka harba makamin igwa zuwa rukunin sojojinsa da ke gudanar da aiki kusa da Kogin Litani. Ɗaya daga cikin harsashin makamin ya fashe kusa da Dagan.

Likitocin fagen fama sun yi ƙoƙarin ba shi taimakon gaggawa a wurin, amma tilas ta sanya suka tabbatar da mutuwarsa.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare. Negev Dagan ya yi aiki ne a Bataliya ta 12 ta Brigade na Golani.

An ƙara masa girma bayan mutuwarsa daga Sergeant zuwa Staff-Sergeant. Dagan shi ne soja na shida da ya faɗi a fagen fama tun bayan da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta ta fara aiki.

Hezbollah ta kai hari kan sojojin Isra'ila

Tashar Aljazeera ta ce tun da farko Hezbollah ta ce ta "kai hari kan taron sojojin makiya na Isra’ila a rukunin Rosh Hanikra [Ras an-Naqoura]" kusa da iyakar Lebanon da jirgi mara matuƙi.

Kara karanta wannan

Ana fargabar harin sojojin sama ya kashe kusan mutane 100 a Zamfara

Dakarun sojojin Isra’ila sun bayyana cewa "farar hula na Isra’ila da dama sun ji rauni kuma an kwashe su domin ba su kulawar likita" bayan wani jirgi mara matuƙi da ƙungiyar ta harba.

Sojan Israila ya mutu a Lebanon
Sojan Isra'ila da aka kashe a Kudancin Lebanon Hoto: @naftalibennett
Source: Twitter

Ana tattaunawa tsakanin Isra'ila, Lebanon

Hakan na zuwa ne yayin da aka fara zagaye na uku na tattaunawa kai-tsaye tsakanin Isra’ila da Lebanon a Washington, DC, kwanaki kaɗan kafin karewar "yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta" wadda kusan ba ta dakatar da hare-haren Isra’ila da martanin Hezbollah gare su ba.

Tattaunawar, wadda aka fara ranar Alhamis, 14 ga watan Mayun 2026, ta samu halartar manyan wakilai daga Lebanon da Isra’ila bayan zaman share fage na farko da jakadun ƙasashen biyu a Washington suka jagoranta.

Isra'ila ta hukunta sojojinta

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Isra'ila (IDF) ta hukunta wasu sojojinta da suka ci mutuncin mutum mutumin mamar Yesu Almasihu.

Rundunar IDF ta ta bayyana cewa ta yanke wa wasu sojoji biyu hukuncin ɗauri a gidan kurkuku bayan kammala bincike kan zargin da ake yi masu.

Ta bayyana cewa yanke hukuncin ne bayan an ɗauki ɗaya daga cikinsu hoto yana sanya tabar sigari a bakin mutum-mutumin mamar Yesu Almasihu a Kudancin Lebanon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng