Nigeria @66: Cikakken Jawabin da Tinubu Ya Yi Wa Yan Najeriya a Ranar Samun Yancin Kai

Nigeria @66: Cikakken Jawabin da Tinubu Ya Yi Wa Yan Najeriya a Ranar Samun Yancin Kai

A yau Alhamis, 1 ga watan Oktoba, 2026, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi wa yan Najeriya jawabi domin murnar cikar Najeriya shekara 66 da samun yancin kai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Shugaba Bola Tinubu ya sake jaddada tasirin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatar a jawabinsa na ranar samun ’yancin kai na ƙarshe kafin babban zaɓen shekara mai zuwa.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tinubu ya soki yan adawarsa

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa cikakken jawabin d Tinubu ya yi a shafinsa na Facebook

Tinubu ya kwatanta Najeriya da mara lafiya mai fama da cutar kansa lokacin da ya karɓi ragamar mulki a 2023, yana mai cewa sai an yi masa magani mai zafi da wahala domin ya samu sauƙi.

Shugaban ƙasar ya kuma soki wasu abokan hamayyarsa da suka ba da shawarar dawo da tallafin mai, inda ya bayyana irin wannan shawara a matsayin “komawa baya”.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da Tinubu ya tabo a jawabin ranar bikin murnar samun ‘yancin kai

Cikakken jawabin da Tinubu ya yi

Ga cikakken jawabin shugaban ƙasar na bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya:

Yan uwana ’yan Najeriya

Shekaru 66 da suka gabata a yau, aka ɗaga tutarmu a karon farko a matsayinnwata ƙasa mai ’yanci da cikakken ikon kanta. Tun daga lokacin, mun yi wannan tafiya tare a matsayin al’umma ɗaya, haɗe da amincewarmu ga babban alkawarin Najeriya: cewa ƙasa mai girmanmu, arzikinmu mai yawa, bambancin al’adunmu da, sama da komai, mutanenmu za su iya gina ƙasa mafi girma a Afirka; cewa a wannan ƙasa mai albarka da yalwar amfanin gona za mu iya gina ƙasa mai haɗin kai, ƙarfi da wadata; ƙasar da ke da muhimmiyar rawa a yankuna da tasiri a duniya.

Tafiyarmu ba ta kasance mai sauƙi a koyaushe ba. A gaskiya, ta kasance mai wahala matuƙa ga mutane da yawa. Mun fuskanci lokutan nasara da kuma lokutan da suka kawo cikas. Mun sha yaƙi, mulkin soja, matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro da rikice-rikicen siyasa. Duk da haka, a cikin dukkan waɗannan, Najeriya, saboda karfin mutanenta da ba ya rushewa, ta jure.

Kara karanta wannan

Duk da korafe korafe, Tinubu ya bayyana nasarorinsa a fannin tattalin arziki

Ta jure ne saboda ƙoƙarin manomin da ke tashi kafin wayewar gari domin ya noma gonarsa. ’Yar kasuwar da ke buɗe shagonta kowace safiya, cike da fatan samun rana mai amfani. Malamin da ya yi imani da yaran da aka damƙa masa amanar kulawa da matashin ɗan kasuwa da ya ƙi barin burinsa saboda yanayin da yake ciki. Muna godiya ga dakaru maza da mata na rundunonin soji da jami’an tsaro waɗanda ke jefa kansu cikin haɗari domin sauranmu mu rayu cikin zaman lafiya.

A cikin kowace irin wahala, ’yan Najeriya sun ci gaba da yin imani da abu guda: cewa wannan ƙasar tamu za ta fi kyau.

Wannan imani, wanda ke tare da mu baki ɗaya, shi ne abin da muka gada daga ’yancin kai. Magabatanmu ba su yi gwagwarmaya ba ne kawai domin tuta, taken ƙasa ko samun matsayi a cikin ƙasashen duniya. ’Yancin kai ya ɗauki wani babban alkawari: cewa ’yan Najeriya za su samu ’yancin tsara makomarsu da kansu tare da gina ƙasa da za ta iya samar da dama, mutunci da rayuwa mafi kyau ga mutanenta. Shekaru 66 bayan haka, Allah Maɗaukaki Ya ɗora mana alhakin cika wannan alkawari.

A yau, yayin da muke bikin samun ’yancin kanmu, dole ne mu yi magana cikin gaskiya kan tafiyar da muka yi zuwa yanzu, zaɓukan da muka yi da kuma ƙasar da muka ƙuduri aniyar ginawa daga nan.

Na tsawon lokaci, alkawarin Najeriya ya kasance yana samun tangarda saboda jinkirta daukar matakai masu wahala, tare da barin gurbacewar tattalin arziki mai zurfi ta ƙara yaɗuwa.

Kara karanta wannan

Kasa za ta yi saiti, Tinubu ya juyo kan abin da ya fi damun yan Najeriya

A shekarar 2023, talauci yana ƙaruwa, kuma fata ya kusan ƙarewa. Halin da ƙasar ke ciki ya yi muni fiye da kowane lokaci. Ba mu da wani zaɓi illa mu ɗauki mataki.

Najeriya ta kasance kamar mara lafiya da aka sanar da shi mummunan labari cewa yana fama da cutar kansa. Likitansa ya bayyana masa cewa maganin zai kasance mai wahala da zafi, amma yana da babbar damar warkewa. Mara lafiyar yana da zaɓi. Zai iya fara magani, ya jure wahalarsa kuma ya yaƙi cutar. Ko kuma ya nemi a ba shi maganin rage radadi kawai, domin rage masa ciwo, ya bar cutar ta ci gaba da yaɗuwa.

Na tsawon lokaci, shugabannin Najeriya sun zaɓi maganin rge radadi yayin da suke addu’ar samun wata mu’ujiza da ba ta taɓa zuwa ba.

Sun mai da hankali kan alamomin cutar yayin da suka bar cutar ta kutsa cikin tsarin al’ummarmu. Mun kashe makudan kuɗaɗe wajen ci gaba da wasu tsare-tsare marasa inganci waɗanda ba a taɓa nufin su dawwama ba. Mun guje wa gaskiyar da ke da wuya, muka riƙa tura sakamakonta daga tsara zuwa tsara.

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Tinubu ya sanar da 'yan Najeriya halin da ya tsinci kasar a 2023

Lokacin da wannan gwamnati ta karɓi mulki, mun ƙuduri aniyar yin abubuwa daban. Mun zaɓi magance cutar kansar. Sauye-sauyen da suka biyo baya sun kasance masu wahala. Illolinsu sun kasance a zahiri. Duk da haka, kada mu taɓa rikita magani da cuta.

Sauye-sauyenmu ba su haifar da raunin tattalin arzikinmu ba. Sun tunkare su ne. Yanzu, yayin da wasu manyan masu ra’ayin komawa baya ke son mu yi watsi da maganin mu koma ga amfani da tallafin da ya zama kamar jaraba, dole ne mu ƙi wannan kira. Dole ne mu tuna dalilin da ya sa muka fara wannan tafiya da kuma nisan da muka riga muka yi.

Bayan shekaru uku da rabi, hujjar cewa yanayin tattalin arzikin Najeriya ya inganta ba za a iya musantawa ba. Tattalin arzikinmu ya samu bunƙasa da sama da kashi 4 cikin 100 a bana. Bangaren mai da wanda ba na mai ba duk sun taimaka wajen kawo mu wannan lokaci na samun ci gaba mai ɗorewa.

Satar mai ta ragu. Hauhawar farashin kayayyaki ta ragu sosai daga matsayinta mafi girma. An sake gina ajiyar kuɗin waje, kasuwar musayar kuɗaɗen waje ta samu daidaito, kuma a 2025 Najeriya ta samu mafi yawan kuɗaɗen shiga daga fitar da kayayyakin da ba na mai ba a tarihinta, wanda ya haura dala biliyan 6. Wannan kuɗi ne na gaske da ’yan kasuwancin Najeriya suka samar.

Kara karanta wannan

2027: Rarara ya sake fitowa da maganganu masu zafi kan 'yan Arewa da Tinubu

Waɗannan ba iƙirarin banza ba ne. Masu sa ido na ƙasa da ƙasa, ’yan jarida, ƙungiyoyi masu zaman kansu da cibiyoyin ƙasa da ƙasa na iya ganin sauyin. Kowannensu ya kammala da cewa sauye-sauyenmu sun ƙarfafa daidaiton tattalin arzikin Najeriya da juriyarta. Kamfanoni masu zaman kansu sun daɗe da bayyana matsayinsu, kuma jarin waje kai tsaye yana ci gaba da ƙaruwa kowace shekara.

’Yan Najeriya ’yan uwana, mun kai wani muhimmin matsayi na sauyi.

Maganin gaggawa ya ƙare. An gyara harsashin ginin tattalin arziki. Babban aikin tattalin arzikin da ke gabanmu ya sauya. Tsawon shekaru uku, babban manufarmu ita ce gyara tafarkin ƙasarmu.

Yanzu, manufarmu mai sauƙi ce: wadata da za ta shafi kowa kuma ta yaɗu.

Lokacin da nake magana kan wadata, ba ina nufin tattalin arziki mafi girma kawai, lambobi marasa ma’ana ko ƙididdiga mafi kyau ba. Ina nufin wani abu da ya shafi rayuwar mutane kai tsaye.

Ina nufin Najeriya inda manomi zai iya noma gonarsa cikin tsaro, ya samar da ƙarin amfanin gona cikin ƙaramin kuɗi kuma ya samu riba mai kyau daga aikinsa. Najeriya inda masana’antu ke samun wutar lantarki mai ɗorewa, ’yan kasuwa za su iya samun rance, kuma matasa za su samu ayyukan yi masu amfani. Najeriya inda abinci da sufuri suke da araha, ilimi yana kusa da kowa, kuma iyalai masu aiki tuƙuru za su iya kallon gaba cikin kwarin gwiwa.

Kara karanta wannan

Hutu ya kare: Shugaba Tinubu ya bar Faransa, ba zai sauka a Abuja ba idan ya dawo Najeriya

Wannan shi ne alkawarin da yanzu dole mu cika.

Babban abin da muka sa a gaba shi ne rage tsadar rayuwa. Za mu cimma hakan ne ta hanyar rage kuɗin samarwa da jigilar abubuwan da ’yan Najeriya ke amfani da su.

Muna da ƙasa da mutane da za su ciyar da kanmu. Don haka gwamnatina ta mayar da hankali wajen faɗaɗa harkar noma ta amfani da injuna da noma a lokacin rani, inganta samun iri da takin zamani, ƙara amfani da injuna a harkar noma gaba ɗaya, da saka jari wajen ajiya da sufuri. Muna ginawa da kammala hanyoyi, layukan dogo da tashoshin jiragen ruwa waɗanda ke haɗa gonaki da masana’antu da kasuwanni.

Manufarmu mai sauƙi ce. Lokacin da manomi ya samar da amfanin gona cikin ƙaramin kuɗi, lokacin da asarar amfanin gona tsakanin gona da kasuwa ta ragu, lokacin da masana’anta ta samu rahusa wjsen samun wutar lantarki, lokacin da mota mai ɗaukar kaya ta isa inda za ta je cikin sauri, kuma lokacin da yanayin kasuwanci ya samar da gasa mai adalci, duk wannan tanadin kuɗi zai kasance cikin farashin kayayyaki a kasuwa.

Kara karanta wannan

'Za a yi babban haɗari idan Tinubu ya bari aka yi faretin 1 ga Oktoba,' Ayodele

Amma wadata ta fi samun kayayyaki masu rahusa. Tana buƙatar ayyukan yi masu amfani.

Najeriya ƙasa ce mai yawan matasa. Miliyoyin matasan Najeriya suna shiga shekarun balaga a kowace shekara cike da basira, kuzari da buri. Alhakinmu shi ne tabbatar da cewa wannan babbar damar yawan matasa ta zama hanyar samar da arziki maimakon tushen yanke ƙauna.

Saboda haka, mun sanya ayyukan yi, kasuwanci da bunƙasar masana’antu a tsakiyar manufofin gwamnatinmu.

Za mu yi amfani da iskar gas ɗinmu wajen samar da wutar lantarki ga sabbin masana’antu. Za mu tallafa wa kamfanonin da ke ƙoƙarin farfado da masana’antu. Za mu faɗaɗa hanyoyin sadarwar zamani zuwa al’ummomin da suka daɗe suna jiran shiga tattalin arzikin zamani. Za mu saka jari wajen koyar da ƙwarewar da ma’aikata ke buƙata tare da tallafa wa ’yan kasuwan Najeriya da ababen more rayuwa da kuɗaɗen da suke buƙata domin bunƙasa harkokinsu.

Ina son ganin ƙarin ’yan Najeriya suna ƙera abubuwa. Ina son ganin ƙarin gonakin Najeriya suna ciyar da biranenmu tare da samar wa masana’antunmu kayayyaki. Ina son ganin ’yan kasuwan Najeriya suna sayar da kayayyakin Najeriya ga duniya baki ɗaya. Ina son ganin matasan Najeriya suna gina manyan kamfanonin fasaha tare da samar da damar aiki ga wasu a nan gida.

Kara karanta wannan

Abba Kabir ya fada wa 'yan Arewa muhimmancin goyon bayan Tinubu

Ina kuma sane cewa miliyoyin ’yan ƙasarmu ba za su iya jiran gobe ba. Wasu iyalan Najeriya har yanzu suna fama a yau domin samun abinci, kuɗin makaranta, kuɗin magani ko kuma kuɗin zuwa wurin aiki. Matsalolinsu ba su fara ne da sauye-sauyen shekaru ukun da suka gabata ba. Wahalar da suke ciki sakamakon shekaru da dama ne na ƙarancin samar da abubuwa, rashin isassun ababen more rayuwa, ƙarancin dama da kuma cibiyoyin da sau da yawa suka gaza tallafa wa waɗanda suka fi buƙatar taimako.

Ba za mu iya warware matsalolin da suka taru mana a cikin shekaru huɗu ba. Amma za mu iya sauya tafarkinsu. Za mu iya gina tattalin arzikin da zai ci gaba da fitar da mutane daga talauci tare da tabbatar da cewa ba a yi watsi da waɗanda ke cikin mawuyacin hali ba.

Shi ya sa muke ƙarfafa tallafin kai tsaye ga gidajen marasa galihu tare da inganta National Social Register domin taimakon ya isa ga waɗanda suke buƙatarsa da gaske.

Shi ya sa asusun NELFUND ke tabbatar da cewa ɗan gidan da ba shi da kuɗi ba zai yi watsi da burin neman ilimi a matakin gaba da sakandare ba saboda iyayensa ba za su iya biyan kuɗin makaranta ba.

Shi ya sa CREDICORP ke bai wa ’yan Najeriya masu aiki damar samun bashi, wanda ke ba mutane damar mallakar motoci, makamashin hasken rana, na’urorin zamani da sauran muhimman kadarori ba tare da sai sun tara kuɗi na tsawon shekaru ba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu za ta ci bashin biliyoyin daloli a bankin duniya

Shi ya sa, tare da haɗin gwiwar jihohi da ƙananan hukumominmu, za mu ci gaba da ƙarfafa kiwon lafiya na matakin farko, ilimin bai ɗaya da muhimman ayyukan gwamnati da ’yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi suka fi dogaro da su. Tun daga 2023, mun biya albashi da fansho a kan lokaci kuma gaba ɗaya. Mun yi wa tsarin fansho na ƙasa gyara domin ya amfani ’yan fansho da waɗanda ke cikin mawuyacin hali.

Waɗannan shirye-shirye ba su ne madadin wadata ba. Gada ne da za su taimaka wa ’yan ƙasarmu a tafiyarsu zuwa gare ta. Manufarmu ba ita ce kawai mu inganta yadda ake yakar talauci ba.

Za mu fatattake shi.

Hakan zai ɗauki lokaci. Zai buƙaci da’a. Zai buƙaci ci gaba mai ɗorewa shekara bayan shekara da samar da miliyoyin damar ayyukan yi masu amfani a faɗin ƙasarmu.

Amma a karon farko cikin shekaru da dama, mun fara wannan aiki daga matsayi mai ƙarfi; tare da tattalin arzikin da aka gyara muhimmin tafarkinsa. Mun fuskanci zaɓukan da suka yi wuya kuma mun aza harsashin wadata mai ɗorewa. Maimakon mu gaza cika alkawarin samar da kyakkyawar makoma ga ’ya’yanmu, lokaci ya yi da za mu gina wannan makomar.

Zamanin sauye-sauye ya kare. Yanzu zamanin wadata ya fara. Zamanin da alkawarin wannan babbar ƙasa zai zama abin da ’yan Najeriya daga kowane ɓangare na rayuwa za su dandana a zahiri.

Kara karanta wannan

Ana batun rashin lafiya, Onanuga ya fadi halin da Tinubu ke ciki a Faransa

Mun yi tafiya cikin shekaru masu wahala tare. Mun tsallake matakai masu wuya tare. Yanzu kuma, dole mu gina ƙasar da waɗannan matakan suka ba mu damar ginawa.

Na yi imani ƙwarai da abin da ke gaba.

Na yi imani da miliyoyin talakawa waɗanda aikinsu, jarumtarsu da jajircewarsu su ne ainihin ƙarfin ƙasarmu a koyaushe. Hanyar da ke gabanmu za ta buƙaci abubuwa da yawa daga gare mu. Amma yanzu muna tafiya a kanta da ƙafafun da suka tsaya da kyau, alkibla bayyananniya da sabon fata ga makomarmu ta bai ɗaya.

Najeriya ta gyara hanyarta. Mun tsallaka namu Bahar Maliya. Wannan ba lokacin waiwaya ba ne. Mu ci gaba tare, da imani da kanmu, imani da ƙasarmu da imani cewa sadaukarwar da muka yi za ta haifar da sakamako mai kyau.

Alkawarin da ke gabanmu shi ne Najeriya mai yalwa; ƙasa inda aka raba wadata ga kowa, inda kowane yaro zai iya yin mafarki fiye da yanayin da aka haife shi a ciki, kuma inda babban alkawarin ƙasarmu zai bayyana a ƙarshe cikin rayuwar mutanenmu.

Makomarmu tana nan, harsashinmu yana da ƙarfi. Alkiblamu a bayyane take. Don haka mu ci gaba. Kada mu waiwaya.

Barka da Ranar ’Yancin Kai, ’yan Najeriya ’yan uwana. Allah Ya albarkace ku baki ɗaya, kuma Allah Ya albarkaci Tarayyar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262