Tashin Hankali: An Kashe Wani Shugaban Jam'iyyar Su Kwankwaso a Arewacin Najeriya
- Wasu mahara sun kashe shugaban jam'iyyar NDC na mazabar Fiidi da ke yankin Makurdi a jihar Benue da ke Arewa ta Tsakiya
- Rahotanni sun nuna cewa an gano Hon. Igbu Job Terhemen a sume bayan an daure shi da igiya tare da yi masa wata allura
- Jam’iyyar NDC ta bukaci hukumomin tsaro su gaggauta binciken domin gano masu hannu a kisan dan siyasan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue, Nigeria - Wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun kashe Hon. Igbu Job Terhemen, shugaban NDC na gundumar Fiidi, da ke Ƙaramar Hukumar Makurdi a Jihar Benue, ranar Laraba.
An ce wasu ’yan daba ake zargi sun kai wa Terhemen hari da misalin ƙarfe 2:00 na dare, inda suka daure shi da igiyoyi, suka yi masa allurar wani abu da ake zargin mai guba ne.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa bayan haka, maharan suka bar shi kusa da gidansa, a yankin NNPC da ke kan hanyar Makurdi zuwa Otukpo.
Rahotanni sun ce an gano shi cikin yanayin suma, inda ya kasa magana ko sadarwa, kafin daga bisani ya rasu.
Yadda aka kashe shugaban NDC
Wani abokin marigayin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa ’yan jarida a Makurdi cewa Terhemen ya bar gidansa da yammacin Talata domin kallon wasan ƙwallon ƙafa a yankin Kanshio, amma bai dawo gida ba.
Ya ce:
“Ya bar gida ne da yammacin Talata domin kallon wasan, kuma ana sa ran zai dawo gida, amma babu wanda ya gan shi. A lokacin da mutane ke ta neman inda yake, sai aka gano shi da misalin ƙarfe 2:00 na dare ranar Laraba a cikin wani daji kusa da gidansa, a sume.
“Abin takaici, ya mutu kafin a samu damar ba shi kulawar lafiya. Abin mamaki shi ne, maharan ba su kwashe wayarsa ba, domin an gano wayar a tare da shi lokacin da aka kai shi ɗakin ajiye gawawwaki.
“Haka kuma akwai wata alama kamar raunin allura a jikinsa, wanda ke nuna cewa maharan na iya yi masa allurar wani abu, sannan suka jefar da shi cikin daji suka bar shi ya mutu.”
NDC ta bukaci bincike
Da yake mayar da martani kan lamarin, Shugaban NDC na Jihar, Ohini Ojegbe, ya bayyana kisan a matsayin “mugun aikin da aka aikata a fili”, tare da kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da bincike kan lamarin.
Ojegbe ya bukaci hukumomin tsaro su kama waɗanda ake zargi da hannu a kisan tare da tabbatar da cewa an gurfanar da su a gaban kotu.
NDC ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, al’ummar Fiidi da kuma mambobin jam’iyyar, tare da addu’ar Allah Ya ba su haƙurin jure wannan rashi.
Mahara sun kashe dagaci a Kano
Kun ji cewa an kashe dagacin kauyen Aujarawar Alkali da ke yankin Gezawa bayan da masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da shu a Kano.
Tun farko dai an yi garkuwa da Alhaji Ahmad ne ranar Talata, 17 ga watan Satumba, 2026, lokacin da wasu ’yan bindiga suka shiga cikingarin da daddare.
Asali: Legit.ng

