Mimiko: Tsohon Gwamnan Ondo Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

Mimiko: Tsohon Gwamnan Ondo Ya Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC

  • Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Ondo ta kara karfi bayan shigowar tsohon gwamna, Olusegun Mimiko zuwa cikinta
  • Tsohon gwamnan na jihar Ondo ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki bayan ya yi murabus daga tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP
  • Olusegun Mimiko ya bayyana cewa rawar da Shugaba Bola Tinubu ke takawa a gwamnati, ta yi tasiri wajen shigowarsa APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Akure, jihar Ondo - Tsohon gwamnan jihar Ondo, Dr. Olusegun Mimiko, ya koma jam’iyyar APC a hukumance.

Olusegun Mimiko ya sauya sheka zuwa APC ne bayan ya yi murabus daga tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP.

Olusegun Mimiko ya koma jam'iyyar APC
Olusegun Mimiko a wajen sauya shekarsa zuwa APC Hoto: Ayekoto Akindele
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban APC na jiha, Hon. Kolawole Babatunde, tare da mabiya jam’iyyar ne suka karɓe shi a garin Ondo ranar Alhamis, 14 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Tsohon IGP, Usman Baba, ya janye daga neman takarar gwamnan Yobe a APC, ya fadi dalili

Meyasa Mimiko ya shiga jam'iyyar APC?

Yayin da yake jawabi ga dandazon magoya bayan jam’iyyar a lokacin sauya sheƙar tasa, Mimiko ya bayyana cewa rawar da Shugaba Bola Tinubu yake takawa ce ta yi tasiri ga shawararsa ta komawa jam’iyya mai mulki, jaridar The Punch ta kawo labarin.

"Akwai abubuwa masu kyau da dama da gwamnati ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu take yi, kuma ko da yake har yanzu akwai sauran jan aiki, na zo ne domin bayar da tawa gudunmawar ga ƙoƙarin da ake yi na ganin Najeriya ta ci gaba da kasancewa a kan tafarkin zaman lafiya, ci gaba, da bunƙasa.”

- Olusegun Mimiko

Yayin da da yawa daga cikin na kusa da Mimiko suka koma APC tun kafin zaɓen gwamnan jihar Ondo da ya gabata, shi dai ya ci gaba da zama a PDP, ko da yake bai cika taka rawar gani sosai ba har zuwa lokacin da ya yi murabus fiye da wata guda da ya wuce.

Kara karanta wannan

'Yan majalisun da suka fice daga APC bayan rasa tikitin takara a 2027

An yi wa Mimiko maraba zuwa APC

Lokacin da yake maraba da Mimiko, Hon. Kolawole Babatunde ya bayyana cewa Mimiko mutum ne mai ra’ayin ci gaba ta kowane fanni, duba da yadda ya nuna bajinta a fannonin lafiya, ilimi, samar da ababen more rayuwa, da sauran fannonin rayuwa da dama lokacin da yake kan mulki da ma bayan ya sauka.

“Mimiko mai ra’ayin ci gaba ne a ko da yaushe, kuma shigowarsa APC kamar ya dawo gida ne."

- Hon Kolawole Babatunde

Olusegun Mimiko ya sauya sheka zuwa ADC
Olusegun Mimiko na jawabi a wajen sauya shekarsa zuwa APC Hoto: Ayekoto Akindele
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa dukkan manufofin Shugaba Tinubu da ƙoƙarinsa na da alaƙa da ci gaba kuma suna samar da sakamako mai kyau wanda ke jan hankalin sauran ’yan Najeriya masu ra’ayin ci gaba.

Fubara ya magantu kan 'batun' barin APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi martani kan rahotannin da ke cewa ya fice daga jam'iyyar APC.

Gwamna Siminalayi Fubara ya tabbatar da cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar APC duk da rade-radin da ake yadawa.

Fubara ya jaddada cewa bai bar APC ba, kuma har yanzu yana nan a matsayin cikakken dan jam’iyyar mai mulki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng