Hakeem Baba Ahmed Ya Tsallake Atiku, Ya Faɗi Dan Takarar da Ya Fi Cancanta a Zaben 2027

Hakeem Baba Ahmed Ya Tsallake Atiku, Ya Faɗi Dan Takarar da Ya Fi Cancanta a Zaben 2027

  • Shugaban PRP, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya yyana Donald Duke a matsayin wanda ya fi sauran ‘yan takara nagarta a zaben shugaban kasa na 2027
  • Amma ya amince cewa cancantar dan takara ita kadai ba ta isa ta sa a samu nasara a zabe ba
  • Jam'iyyar PRP na taka muhimmiyar rawa a kokarin gina kawancen jam’iyyun adawa gabanin zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja, Nigeria - Shugaban jam’iyyar PRP, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya ce dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Donald Duke, shi ne ya fi kowane dan takara cancanta a zaben 2027.

Ya ce Duke, tsohon gwamnan Cross River yana da nagarta da cancantar jagorantar Najeriya fiye da sauran masu neman kujerar shugaban kasa kamar Atiku Abubakar, Peter Obi da Bola Tinubu.

Donald Duke.
Dan takarar shugaban kasa n jam'iyyar PRP a zaben 2027, Donald Duke Hoto: Donald Duke
Source: Facebook

Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise News ranar Laraba, 30 ga watan Satumba, 2026.

Baba Ahmed ya zabi dan takara 1

Kara karanta wannan

Atiku ya buƙaci Tinubu ya saki El Rufai, Sheikh Zaria, ya taɓo batun Nnamdi Kanu

Ya ce:

“Idan aka dora yan takara a ma'suni, muna ganin muna da mafi cancanta. Mun yi sa’ar samun sa. Don haka, idan aka kwatanta dan takara da dan takara, Donald Duke ya fi dukkan ‘yan takarar da ke wajen.”

Sai dai ya kara da cewa PRP ba ta dogara kacokan kan cancantar Duke wajen kai jam’iyyar ga nasara ba, yana mai cewa wannan fahimtar ce ta sa jam’iyyar ke taka rawa sosai a tattaunawar da ake yi kan kafa kawancen adawa gabanin zaben.

“Sai dai muna da cikakkiyar fahimtar cewa cancantar dan takara kadai ba ta wadatar wajen lashe zabe, shi ne dalilin da ya sa PRP ke sahun gaba, a tsakiyar kokarin gina wannan kawance.”

PRP na neman kawancen jam’iyyu

Baba-Ahmed ya bayyana cewa kokarin PRP na samar da kawance tsakanin jam’iyyun adawa yana karkashin jagorancin cimma matsaya da bin hanyoyin da kundin tsarin mulki ya tanada.

A rahoton Vanguard, shugaban PRP ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Kotu ta soke zaben fitar da gwani na jam'iyyar APC a jihar Gombe

“Ba ma son mu riga mu yanke hukunci ko mu yi wa komai katanga ta hanyar cewa, ‘Saboda shi ne mafi cancanta, dole ya zama dan takara,’ ta kowace hanya da za a bi wajen cimma hakan. Muna son gina kawancen jam’iyyun da ke da ra’ayi irin namu.”

Ya jaddada cewa hadarin da ke tunkaro wa a zaben 2027 ya fi bukatun jam’iyya girma, yana mai bayyana zaben a matsayin wani muhimmin lokaci da zai tantance alkiblar Najeriya.

Hakeem Baba Ahmed.
Shugaban jam'iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed Hoto: Hakeem Baba-Ahmed
Source: UGC

Jawabin shugaban PRP ya zo ne a daidai lokacin da kokarin gina kawance tsakanin jam’iyyun adawa ke kara karfi gabanin zaben shugaban kasa na 2027, inda Duke yake daga cikin fitattun mutanen da irin wannan kawance zai iya karkata zuwa gare su.

Okonkwo ya shawarci yan adawa

A wani labarin, kun ji cewa Kenneth Okonkwo ya yi gargaɗin cewa rashin haɗin kan ‘yan adawa a bayan ɗan takara guda na iya ƙara wa Shugaba Bola Tinubu ƙarfi a zaɓen 2027.

Mai magana da yawun kwamaitin kamfen Atiku ya ce ‘yan adawa za su iya fuskantar jam’iyyar APC da ƙarfi ne kawai idan suka haɗa tsarin siyasarsu a bayan dan takara daya.

Okonkwo ya gina hujjarsa ne a wani ɓangare kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023, lokacin da kuri’un manyan ‘yan takarar adawa suka rabu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262