Atiku Ya Buƙaci Tinubu Ya Saki El Rufai, Sheikh Zaria, Ya Taɓo batun Nnamdi Kanu

Atiku Ya Buƙaci Tinubu Ya Saki El Rufai, Sheikh Zaria, Ya Taɓo batun Nnamdi Kanu

  • Atiku Abubakar ya bukaci Bola Tinubu ya magance korafe-korafen Nnamdi Kanu da ke tsare a gidan yari
  • Ya kuma soki tsawaita kasafin 2025 zuwa karshen 2026, yana cewa hakan na bukatar gwamnati ta bayyana abin da aka kashe
  • Dan takarar ADC ya ce tsadar rayuwa ta kara tsananta, yayin da ya yi alkawarin rage farashin man fetur da sufuri idan aka zabe shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya shawarci Bola Tinubu kan lamarin Malam Nasir El-Rufai.

Atiku ya bukaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta magance korafe-korafen jagoran masu neman kafa Biafra, Mazi Nnamdi Kanu, wanda aka samu da laifi.

Atiku ya caccaki Tinubu kan tsare Kanu, El-Rufai da Sheikh Khalifa Zaria
Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar. Hoto: Bayo Onanuga, Atiku Abubakar.
Source: Twitter

Atiku ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis a Abuja yayin jawabinsa na ranar samun ‘yancin kan Najeriya wanda ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da Tinubu ya tabo a jawabin ranar bikin murnar samun ‘yancin kai

Atiku ya yi jawabi kan ranar 'yancin kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma bukaci gwamnati ta yi bayani kan ci gaba da tsare Sheikh Sani Khalifa Zaria da Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, yana cewa lamarin ya haifar da tambayoyi kan bin ka’idojin shari’a.

Ya ce:

“A wannan rana, ina kira da a yi amfani da tsarin doka cikin adalci a kowane lamari. Ci gaba da tsare Sheikh Sani Khalifa Zaria da Mallam Nasir Ahmad El-Rufai na haifar da tambayoyi kan tsarin shari’a.”

Game da Kanu, Atiku ya ce bayan samun hukuncin kotu, ya kamata a mutunta hakkinsa na daukaka kara bisa doka, tare da magance korafe-korafe da rarrabuwar kawuna da lamarin ya haifar.

Atiku ya sake yin kira da a saki matasan Najeriya biyar da aka kama a Borno bayan sun sanya rigunan da aka rubuta “Tinubu Must Go”, wato “Tinubu ya tafi”.

Yayin bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kan Najeriya, Atiku ya ce kasar ta yi nisa da hangen nesan wadanda suka kafa ta, yayin da shekaru uku na gwamnatin Tinubu suka kara tsananta wahalhalun jama’a.

Kara karanta wannan

'Babbar masifar da Arewa za ta fuskanta idan Atiku ko Obi suka lashe zaɓen 2027'

Atiku ya dura kan gwamntin Tinubu a Najeriya
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Getty Images

'Kuskuren da Tinubu ke yi' - Atiku

Atiku Abubakar ya ce Shugaba Tinubu na tafiyar da gwamnati ne bisa alkawura maimakon abin da aka samu a aikace, yana kalubalantar ikirarin shugaban cewa lokacin matsalar gaggawa ya wuce kuma zamanin wadata ya fara.

Ya ce:

“Shekaru uku da suka gabata karkashin Bola Tinubu sun jefa Najeriya cikin mafi tsananin matsalar tsadar rayuwa a tarihinmu. Iyali na rage abinci, jinkirta neman magani da karbar bashi domin su tsira.
"Shugaba na iya sanar da sabon babi a cikin jawabi, amma ba zai iya sanya abinci a teburin iyali ko kudi a aljihun ma’aikaci ba.”

Dan takarar ADC ya kuma soki tsawaita amfani da kasafin kudin shekarar 2025 har zuwa karshen shekarar 2026, yana neman gwamnati ta bayyana yadda aka kashe kudaden da kuma ayyukan da aka kammala.

Tinubu ya fadi yadda ya samu Najeriya

An ji cewa Bola Tinubu ya kwatanta Najeriya ta 2023 da mara lafiya da ke bukatar magani mai wahala domin samun damar murmurewa.

Kara karanta wannan

Shirin Bola Tinubu na tsaka mai wuya da APM ta aika saƙo na musamman Bankin Duniya

Shugaban ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa sun tunkari matsalolin da suka dade suna addabar tattalin arzikin Najeriya.

Tinubu ya ce Najeriya ta kai wani mataki na sauyi, kuma gwamnati yanzu ta mayar da hankali kan samar da wadata ga jama’a baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.