Shirin ISWAP Ya Rushe, Bam Ya Hallaka Abu Umar da Wasu Manyan Yan Ta'adda 5 a Borno

Shirin ISWAP Ya Rushe, Bam Ya Hallaka Abu Umar da Wasu Manyan Yan Ta'adda 5 a Borno

  • Bam ya tashi da wasu manyan 'yan ta'adda na kungiyar ISWAP kafin lokacin da suka shirya tashinsa a karamar hukumar Marte ta jihar Borno
  • Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a safiyar yau Asabar yayin da 'yan ta'addan ke kokarin hada bam a yankin Jubilaram
  • Wannan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan sojojin Najeirya da na Amurka sun kashe Abu Mainok, wani babban kwamandan ISIS a tafkin Chadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Akalla mutane shida da ake zargin ‘yan ta'addan kungiyar ISWAP ne sun mutu bayan bam ya tarwatse kafin lokacin da aka shirya a karamar hukumar Marte da ke jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na safiyar ranar Asabar, 16 ga Mayu, 2026, a yankin Jubilaram, inda ake zargin ‘yan ta’addan na kokarin dasa bam din.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana bayan Amurka ta yi ikirarin kashe kasurgumin dan ta'adda a Najeriya

Borno.
Taswirar jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Vanguard ta ce wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan hadin gwiwar sojojin Amurka da na Najeriya sun kashe daya daga cikin manyan kwamandojin ISWAP da ke aiki a yankin Tafkin Chadi.

Bam ya tashi da yan ta'adda a Borno

Majiyoyin sun ce tawagar masu hada bam din tana karkashin jagorancin wani kwararren mai kera bama-bamai da ake kira Abu Umar, wanda shi ma ya mutu a fashewar tare da wasu mayaka biyar.

Rahotanni sun kuma ce wasu mutum uku daga cikin kungiyar sun samu munanan raunuka sakamakon lamarin.

Binciken bayanan sirri ya nuna cewa wadanda suka mutu na daga cikin kwamandoji a sashen masu hada bama-bamai na kungiyar ISWAP da ke aiki a yankin Marte–Kerenoa–Wulgo.

Ana kyautata zaton cewa fashewar ta faru ne yayin da ake hada bam din lamarin da ya jawo ya tashi kafin lokaci tare da lalata wurin da kuma haddasa asarar rayuka da dama.

Kara karanta wannan

Yadda harin sojojin sama ya hallaka farar hula da 'yan ta'adda a Zamfara

Bam ya yi wa kungiyar ISWAP illa

Mutuwar Abu Umar da sauran kwararrun masu hada bama-bamai na iya kawo cikas sosai ga ayyukan kungiyar na amfani da bama-bamai a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya shafi wata cibiyar hada bama-bamai da ke tsakanin Arinna Maimasallaci da Arinna Ciki, wadda ake zargin yanzu ta daina aiki na wani lokaci.

Sojoji.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya a tsakiya daji yayin da suke kokarin tabbatar da zaman lafiya a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Majiyoyin soji sun ce wannan ci gaba na iya kara raunana karfin ayyukan kungiyar ISWAP a muhimman hanyoyin yankin Marte, kamar yadda Zagazola Makama ya wallafa a X.

Hukumomin tsaro na kuma duba yiwuwar kaddamar da karin hare-haren sama da na kasa domin cin gajiyar halin da kungiyar ta shiga tare da hana ‘yan ta’addan ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankin.

Bam ya tarwatse da manoma a Borno

A wani labarin, kun ji cewa wani bam da ake zargin mayakan Boko Haram suka dasa, ya tashi da manoma, masu kamun kifi da masu zuwa yin itace a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Kawancen PDP da APM: Gwamna Makinde zai ayyana shiga takarar shugaban kasa a 2027

Akalla mutane 20 da suka hada da masu kamun kifi da masu sare itace sun mutu sakamakon tashin bam din da ya rutsa da su kusa da garin Gwoza.

Harin ya ƙara nuna irin barazanar da manoma da mazauna karkara ke fuskanta a yankunan da ke fama da matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262