Gwamnatin Tinubu Ta Yi Magana kan Maido Tallafin Mai a Ranar 'Yanci
- Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da yiwuwar dawo da tsarin tallafin man fetur, tana mai cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ya yi sun zama dole domin ceto Najeriya
- Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya bayyana cewa gwamnati ba za ta koma tsarin tallafin da ya gabata ba, yayin da ya yi bayani kan nasarorin da aka samu
- Akume ya kuma ce tattalin arzikin Najeriya ya bunƙasa da kashi 4.2 cikin 100 a watannin farko na 2026, daga kashi 3.9 cikin 100 a makamancin lokacin shekarar 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba za ta dawo da tsarin tallafin man fetur ba, tana mai cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar sun zama dole domin ceto ƙasar daga durƙushewa.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu saboda cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yanci
Rahoto ya nuna cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abuja yayin lacca ta cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.

Source: Facebook
Maganar tallafin man fetur
Vanguard ta wallafa cewa Akume ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai masu tsauri tun bayan da ta karɓi mulki a 2023, ciki har da cire tallafin man fetur, haɗa kasuwar musayar kuɗin waje da sauye-sauyen haraji da sauran manufofin kuɗi.
Ya ce waɗannan matakai sun kasance masu wahala, amma sun zama dole domin sake samar da daidaito a tattalin arzikin ƙasar.
A cewarsa, gwamnati ba za ta koma tsarin tallafin man fetur da ya gabata ba duk da bukatar da 'yan kasar ke nunawa.
Bunƙasar tattalin arziki
Akume ya ce bayanan Bankin Duniya sun nuna cewa GDP na Najeriya ya bunƙasa da kashi 4.2 cikin 100 a rabin farko na 2026, daga kashi 3.9 cikin 100 a shekarar da ta gabata.
Ya ce babban abin da ke gaban gwamnati yanzu shi ne tabbatar da cewa bunƙasar tattalin arzikin ta haifar da ƙarin ayyukan yi da kuma kuɗin shiga ga ’yan Najeriya.
Punch ta wallafa cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya ya kuma ce sauya amfani da man fetur zuwa iskar gas na taimakawa wajen rage kuɗin sufuri da makamashi.
Ya bayyana cewa an sauya motoci sama da 120,000 zuwa amfani da CNG, yayin da ake da cibiyoyin sauya motoci sama da 400 da tashoshin cike CNG 90 a faɗin ƙasar.

Source: Facebook
Maganar tazarcen Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa Leke Abejide ya ƙaddamar da shirin wayar da kan al’umma da tallafa wa Yarbawa miliyan daya a faɗin jihar Kano domin neman goyon bayansu ga Shugaba Bola Tinubu.
Abejide, wanda ke wakiltar mazaɓar Yagba ta Tarayya a jihar Kogi, ya ƙaddamar da shirin ne bayan kafa kwamiti mai mutum 27 da zai gudanar da ayyukan a ƙananan hukumomin Kano 44.
Ya ce shirin zai mayar da hankali kan zawarawa, matasa, mata, ’yan kasuwa, masu rauni da sauran mutanen da ke buƙatar tallafin tattalin arziki.
Asali: Legit.ng
