Kaico: Yan Bindiga Sun Kashe Basarake a Wani Yanayi Mai Ban Tausayi a Jihar Kano

Kaico: Yan Bindiga Sun Kashe Basarake a Wani Yanayi Mai Ban Tausayi a Jihar Kano

  • An kashe dagacin kauyen Aujarawar Alkali da ke yankin Gezawa bayan da masu garkuwa da mutane suka yi awon gaba da shi
  • Rahotanni sun nuna cewa an gano gawar Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad a wani kabari mara zurfi bayan kwanaki huɗu
  • Wasu bayanai sun nuna cewa yan bindigan sun azabtar basaraken bayan sun yi garkuwa da shi kafin su kashe shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - An ruwaito cewa yan bindiga sun kashe magajin garin kauyen Aujarawar Alkali da ke Ƙaramar Hukumar Gezawa a Jihar Kano, Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad.

Tun farko dai an yi garkuwa da Alhaji Ahmad ne ranar Talata, 17 ga watan Satumba, 2026, lokacin da wasu ’yan bindiga suka shiga cikin garin da daddare tare da yin awon gaba da shi.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun kashe wani matashi mai shayi a jihar Adamawa

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An gano gawar dagacin kauye a Kano

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa an gano gawar basaraken ne bayan masu garkuwar sun kashe shi kuma tuni aka gudanar da sallar jana’izarsa da ƙarfe 3:00 na rana ranar Laraba.

Musa Garba, wani mazaunin Gezawa, ya tabbatar da lamarin ga wakilinmu ta wayar tarho.

A cewarsa, maharan sun azabtar da basaraken har ya mutu, inda suka yanke ɗaya daga cikin ƙafafunsa sannan suka ɗaure hannayensa.

Garba ya ce daga bisani masu garkuwar sun binne gawar Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad a wani rami mara zurfi a wani ƙauye mai suna Danladin Gezawa.

Yadda maharan suka kashe basarake

Magidancin ya tabbatr da cewa da shi aka yi wa gawar basaraken jana'iza inda daga bisani aka sake birne shi a makabarta

Musa Garba ya ce:

“Na halarci sallar jana’izar yau (Laraba) da misalin ƙarfe 3:00 na rana. Yan ta'addan sun azabtar da mai garin har ya mutu, inda suka yanke ɗaya daga cikin ƙafafunsa tare da ɗaure hannayensa a bayansa.

Kara karanta wannan

An cafke matashi mai tsaron dazuka da aka dauka da alaka da yan bindiga

"Alamu sun nuna cewa haka suka ci gaba da azabtar da shi har ya mutu. Bayan rasuwarsa, masu garkuwar sun birne gawarsa a wani rami mara zurfi a wani ƙauye mai suna Danladin Gezawa.
"Bayan kwanaki huɗu da yin garkuwa da shi, wasu mazauna ƙauyen suka gano ramin tare da sanar da jama'a, aka zo aka tono gawar aka dauko ta."

Ya ce matar magajin garin ta samu ganin gawar kafin a wuce da ita zuwa asibiti domin tabbatrwa da kuma gwaje-gwaje.

“Matar marigayin ce ta gane gawar. An kai ta asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarsa, daga bisani jami’an asibitin suka jagoranci birne shi saboda gawar ta riga ta fara ruɓewa.”

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ’yan sanda ba su fitar da sanarwar hukuma kan lamarin ba.

Yan bindiga sun sace mutane 75

Kun ji cewa an sace akalla mutane 75 a sababbin hare-haren da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a Bungudu da wasu kauyuka a Zamfara.

Wani mazaunin garin Bungudu mai suna Abdurrazaq ya ce ana zargin ’yan bindigar sun kai harin ne domin sake sace shugaban Karamar Hukumar Bungudu, wanda bai dade da kubuta daga hannunsu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262