Jigon ADC Ya Ragargaji Kwankwaso da Obi, Ya Fadi Dalilinsu na Komawa NDC
- Ana ci gaba da magana kan matakin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi suka dauka na ficewa daga jam'iyyar ADC
- Wani mamba a kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na ADC, Kenneth Okonkwo, ya fito ya ragargaji 'yan siyasar guda biyu
- Kenneth Okonkwo ya bayyana cewa duk wanda ya fice daga tafiyar hadaka, yana taimakawa Shugaba Bola Tinubu ne don sake lashe zabe a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani mamba a kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar ADC, Kenneth Okonkwo, ya soki Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Kenneth Okonkwo ya soko tsofafffin gwamnonin ne kan shawararsu ta barin haɗakar jam’iyyar ADC zuwa jam’iyyar NDC.

Source: Facebook
Kenneth Okonkwo ya yi sukar ne yayin wata tattaunawa a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv a ranar Alhamis, 14 ga watan Mayun 2026.
Me jigon ADC ya ce kan Kwankwaso, Obi?
Dukansu fitattun ’yan adawar biyu sun fita daga haɗakar jam’iyyun da ke ƙarƙashin inuwar ADC kwanan nan don komawa NDC, matakin da Okonkwo ya bayyana a matsayin rashin gaskiya.
“Bari na faɗa cewa su ’yan damfarar siyasa ne. Ina magana ne kan Peter Obi da Kwankwaso."
“Su da kansu suka shigo cikin haɗakar nan, kuma suka ce haɗaka ita ce hanya mafi kyau kuma guda ɗaya tilas ta korar Tinubu kamar yadda suka faɗa da bakunansu, sannan su da kansu ba tare da wani dalili ba suka fita zuwa NDC, shin hakan ba damfara ba ce?”
- Kenneth Okonkwo
Okonkwo ya kawo dalilinsu na barin ADC
Okonkwo ya yi zargin cewa Obi da Kwankwaso sun bar ADC ne saboda ba su shirya gudanar da zaɓen fitar da gwani a cikin jam’iyyar ba.
A cewarsa, duk wanda ya bar haɗakar ADC to yana bayar da goyon baya ne a fakaice ga sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sai dai ya nanata cewa ficewar Obi da Kwankwaso ba za ta yi wani babban tasiri ga manufar haɗakar na kawar da jam’iyya mai mulki a shekarar 2027 ba.
Za a ga sauyi a 2027
Jigon na ADC ya kuma yi ikirarin cewa shiyyoyin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu za su kaɗa ƙuri’a a 2027 ta hanyar da za ta taimaka wa haɗakar jam’iyyun.
Ya ce yankunan biyu za su haɗe da haɗakar jam’iyyun da kuma yankin Arewa domin zaɓar wanda ba Tinubu ba.
“Tun daga 2015 lokacin da Goodluck Jonathan ya faɗi zaɓe saboda Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas, shugabannin da suka biyo baya sun mayar da su saniyar ware saboda ba su tafi tare da su ba."
“A 2027, yankin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas za su haɗe da haɗaka tare da Arewa, kuma idan suka haɗe, za su doke Tinubu, kuma idan suka doke Tinubu, duk wannan mayar da mutane saniyar ware za ta zo ƙarshe."
- Kenneth Okonkwo

Source: Twitter
Kwankwaso, Obi sun yi yunkurin shiga PRP
A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi sun yi yunkurin shiga jam'iyyar PRP mai adawa.
Shugaban PRP na kasa, Dr Hakeem Baba Ahmed ya bayyana cewa sun tattauna da manyan 'yan siyasar, amma daga karshe ba a samu matsaya ba.
Baba Ahmed ya ce tattaunawar da aka yi tsakanin PRP da jiga-jigan ta tsaya ne saboda wasu sharuddam da suka gabatar kafin shiga jam’iyyar.
Asali: Legit.ng


