Babbar Magana: Wike Ya Fadi Abin da Zai Sa Ya Yi Murabus a Gwamnatin Tinubu
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana abin da zai saka shi ya yi murabus daga mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- Wike ya ce zai sanar da murabus dinsa ranar 17 ga Janairun 2027, idan Tinubu bai samu nasara a Abuja da Rivers ba a zaɓen shugaban ƙasa
- Ministan ya bayyana cewa yana jagorantar haɗin gwiwar jam’iyyu a Abuja domin samun nasara, tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana abin da zai sa sauka daga mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Wike ya ce zai yi murabus ne idan Tinubu bai samu nasara a Abuja da Rivers a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.
Hakan na cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Yaɗa Labarai da Kafofin Sada Zumunta, Lere Olayinka, ya fitar ranar Laraba.
Ya ce ci gaba da kasancewarsa minista ya danganta da iya samar da sakamakon siyasa ga shugaban ƙasa a wuraren da yake da tasiri.
Ministan ya ce idan jam’iyya mai mulki ta sha kaye a Abuja da Rivers a zaɓen shugaban ƙasa da aka tsara gudanarwa ranar 16 ga Janairun 2027, zai miƙa takardar murabus dinsa washegari.
Wike ya ce:
“Idan ba zan iya kawo nasara a inda nake aiki ba, to ban cancanci kasancewa a nan ba.
“Idan na rasa Abuja, bai kamata in kasance Ministan Abuja ba. Zuwa ranar 17 ga Janairu, 2027, zan sanar da murabus dina a matsayin Ministan Abuja idan Shugaban ƙasa ya sha kaye a Rivers da Abuja.”
Dabarun Nyesom Wike a siyasar Najeriya
Da yake bayyana dabarunsa na siyasa a babban birnin tarayya, Wike ya ce gwamnatin na gina haɗin gwiwar jam’iyyu da nufin samun nasara a kujerun zaɓe daban-daban a Abuja.
Ya bayyana goyon bayansa ga ’yan takara a matakai daban-daban na majalisa, tare da jaddada cikakken goyon bayansa ga ƙoƙarin Tinubu na sake tsayawa takara.
Wike ya ce:
“Mu bayyana matsaya a sarari: A Shugabancin ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne! A Majalisar Dattawa, Philip Aduda mutum ne na jama’a, sabanin waɗanda ke bayyana a talabijin kawai. ’Yan takarar Majalisar Wakilai biyu da muke goyon baya suna nan. Su ne tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi.
“A Abuja, muna gudanar da haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyu domin samar da sakamako.”
Shugabannin APC sun dura kan Wike
Mun kawo rahoton cewa wasu shugabannin APC na jihohi sun yi watsi da kungiyar Rainbow Coalition da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke jagoranta.
Shugabannin jam’iyyar sun bukaci Wike ya koma APC a hukumance idan da gaske yake goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Sai dai wasu sassan APC sun ce za su marabci Wike idan ya koma jam’iyyar, yayin da wasu suka ce ba za su amince da tsarin da zai raba kai ba.
Asali: Legit.ng

