Ku Zo Ku Nema: Rundunar Sojojin Ruwa Ta Bude Shafin Daukar Sababbin Ma'aikata

Ku Zo Ku Nema: Rundunar Sojojin Ruwa Ta Bude Shafin Daukar Sababbin Ma'aikata

  • Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta sanar da fara ɗaukar sabbin ma’aikata na Batch 39 na Makarantar Horas da Sojojin Ruwa ta Najeriya
  • Za a fara neman aikin a ranar 2 ga Oktoba, kuma za a rufe shafin neman aikin ranar 31 ga Oktoba, 2026
  • Neman aikin kyauta ne, kuma Rundunar Sojin Ruwa ta gargaɗi jama’a kada su biya wani mutum da ya yi ikirarin zai taimaka musu samun aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta sanar da fara ɗaukar sababbin ma’aikata domin Batch 39 na Nigerian Navy Basic Training School na shekarar 2026.

Rundunar ta sanar da hakan ne a cikin ƙa’idojin neman aikin da ta wallafa a ranar Litinin, 28 ga watan Satumban 2026.

Za a dauki sababbin sojojin ruwa
Jami'an sojojin ruwa na atisaye Hoto: Nigerian Navy
Source: Facebook

Rundunar sojojin ruwan ta Najeriya ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta sanya a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu za ta ci bashin biliyoyin daloli a bankin duniya

Yaushe za a fara neman aikin?

A cewar Rundunar Sojin Ruwa, za a fara neman aikin daga ranar 2 ga Oktoba zuwa 31 ga Oktoba, 2026.

An bayyana cewa neman aikin kyauta ne kuma dole ne duk masu neman aikin su cika fom ɗin neman aikin ta intanet.

Wadanda suka cancanta za su buƙaci cike dukkan bayanan da ake buƙata tare da tabbatar da cewa bayanan da suka gabatar sun kasance cikakku kuma daidai.

Yadda za a nemi aikin

Masu sha’awar neman aikin za su iya shiga shafin ɗaukar ma’aikatan Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya domin cike fom ɗin neman aikin ta intanet.

Rundunar ta jaddada cewa babu wani kuɗi da ake karɓa wajen neman aikin ko gudanar da wani mataki na aikin ɗaukar ma’aikatan.

Ta kuma gargaɗi masu neman aikin da kada su biya wasu mutane da ke ikirarin za su taimaka musu wajen samun aikin.

“Rajistar intanet da sauran matakan ɗaukar ma’aikata kyauta ne, kuma bai kamata a biya kowa wani kuɗi a kowane mataki na wannan aikin ɗaukar ma’aikata ba,” in ji Rundunar Sojin Ruwa.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 7 da Najeriya ta nema a taron UNGA karo na 81

Waɗanne sharuɗɗa ake buƙata?

Rundunar ta ce masu neman aikin dole ne su kasance marasa aure kuma wadanda aka haifa a Najeriya.

Haka kuma, dole ne su kasance suna da Katin Shaidar Ɗan Ƙasa (National Identity Card), NIN slip ko BVN.

Dole ne masu neman aikin su kasance cikin ƙoshin lafiya ta fuskar jiki da tunani, tare da cika ƙa’idojin lafiyar da ake buƙata a aikin soja.

Bugu da ƙari, ba za a amince da wanda kotu ta taɓa yanke wa hukuncin aikata laifi ba.

Tsawo da shekarun masu neman aikin

Masu neman aikin maza dole ne tsawonsu ya kai aƙalla mita 1.69, yayin da mata kuma dole tsawonsu ya kai mita 1.65.

Haka kuma, dole ne shekarun mai neman aikin su kasance tsakanin 18 zuwa 22 kafin ko a ranar 31 ga Disamba, 2026.

Takardun karatu da ake buƙata

Masu neman aikin dole ne su samu aƙalla 'credit' biyar, ciki har da Lissafi da Turanci, a jarabawar WASSCE, GCE, NECO ko NABTEB.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: EFCC ya ayyana sake neman Abdulrashid Maina ruwa a jallo, ta fadi dalili

Ba za a karɓi sakamakon da aka samu a sama da zama biyu ba.

Ga masu neman aikin tradesmen/tradeswomen, baya ga waɗannan sharuɗɗan, dole ne su kasance da TRADES TEST ko CITY AND GUILDS CERTIFICATE.

Rundunar ta ce ana iya samun ƙarin bayanai kan nau’o’in sana’o’in da ake buƙata da sauran sharuɗɗa a shafin neman aikin.

Za a dauki sojojin ruwa
Wasu jami'an rundunar sojojin ruwa ta Najeriya Hoto: Nigerian Navy
Source: Facebook

Sojoji sun cafke kwamandan 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar Operation Fansan Yamam tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai sun kama wasu manyan kwamandojin wata ƙungiyar ’yan ta’adda a Katsina.

Kungiyar 'yan ta'addan ana alakanta da sacewa da kashe Manjo Janar Abubakar Rabe mai ritaya a Jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng