Ta Tabbata Mutane Sun Mutu a Hannun NSCDC, Gwamna Bago Ya Fadi Halin da Ake ciki
- Gwamnan Neja Umar Bago ya tabbatar da mutuwar mutane 37 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba yayin da suke tsare a hannun NSCDC
- Gwamnatin jihar ta kafa kwamitin bincike, yayin da aka dakatar da kwamandan NSCDC na Neja da tawagarsa domin gudanar da bincike mai zaman kansa
- Ana gudanar da gwaje-gwajen likitanci da na ƙwaƙƙwafi da binciken gawarwaki domin gano ainihin musabbabin mutuwar mutanen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Gwamnan Jihar Neja, Umar Bago, ya tabbatar da mutuwar mutane 37 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba yayin da suke tsare a hannun hukumar NSCDC a Minna.
Gwamnan ya tabbatar da lamarin ne ranar Alhamis, 17 ga watan Satumban 2026 yayin wani taron manema labarai a Minna, inda ya bayyana mutuwar a matsayin abin “tausayi” da “mummunan lamari.”

Source: Twitter
Gwamnati ta kafa kwamitin bincike
Bago ya ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamitin bincike domin gano abubuwan da suka faru da kuma dalilin da ya jawo mutuwar mutanen, cewar rahoton tashar Channels tv.
Ya kuma bayyana cewa an dakatar da kwamandan NSCDC na Jihar Neja da tawagarsa domin ba da damar gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
“Abu mafi muhimmanci shi ne mutane sun mutu a hannun hukumar NSCDC. An tsare su a ɗakuna, kuma da safiyar yau muka wayi gari da labarin cewa 37 daga cikinsu sun mutu,” in ji Bago.
Ba a gano musabbabin mutuwar ba
Gwamnan ya ce har yanzu ba a tabbatar da ainihin abin da ya haddasa mutuwar mutanen ba, yana mai cewa lokaci bai yi da za a yanke hukunci kan musabbabin lamarin ba.
Ya ce masu bincike na duba yiwuwar cewa cunkoso a ɗakin da aka tsare mutanen ya haddasa ƙarancin iska ko kuma mutanen sun fuskanci gubar sinadarai da ake amfani da su wajen haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.
“Mai yiwuwa ya faru ne saboda rashin isasshen iska, domin mutane sun yi yawa a ɗaki guda. Abu na biyu kuma na iya kasancewa sakamakon gubar sinadarai kamar gubar dalma ko wasu sinadarai masu haɗari da ake amfani da su wajen haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba,” in ji shi.
Ana gudanar da binciken likitanci
Bago ya bayyana cewa ana gudanar da gwaje-gwajen ƙwaƙƙwafi, na likitanci da binciken gawarwaki domin gano musabbabin mutuwar a kimiyyance.
Ya kuma ce kwamitocin da NSCDC, Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya da Darakta-Janar na Hukumar DSS suka kafa na gudanar da bincike kan lamarin, baya ga kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa.
Ana binciken kan gawarwakin
Gwamnan ya ce masu bincike suna duba wasu rahotanni da aka samu kan halin da gawarwakin suke ciki.
Daga cikin abubuwan da ake bincike akwai rahotannin cewa wasu daga cikin mamatan sun samu barewar fata, yayin da wasu kuma ake zargin sun yi amai ko kumfar baki da jini.
Sai dai Bago ya yi gargaɗin cewa bai kamata a yanke hukunci kan musabbabin mutuwar ba har sai an kammala binciken ƙwaƙƙwafi da na likitanci.
Ya ce sakamakon binciken ne kawai zai tabbatar da abin da ya haddasa mutuwar mutane 37 ɗin da ke tsare a hannun NSCDC.

Kara karanta wannan
Sokoto: Sunayen malamai da za su tantance kalaman Sheikh Musa Lukuwa kan Annabi SAW

Source: Original
Abin da ya jawo mutuwar mutane a NSCDC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani wanda ya tsira da rayuwarsa ya yi zargin cewa waɗanda suka mutu sun shaƙe ne bayan an cunkushe su a wani ɗaki da ba shi da isasshen iska.
A cewarsa, waɗanda abin ya shafa sun yi ta ihu da kuka suna neman iska, tare da yawan bugun wurin suna kiran a taimaka musu, amma jami’an da ke bakin aiki suka yi watsi da kukansu.
Asali: Legit.ng

