Amaechi Ya Faɗi Sharaɗin Yin Murabus a Gwamnatin Atiku bayan Sun Yi Nasara a 2027
- Rotimi Amaechi ya ba da wa'adin lokacin da da zai yi murabus idan Najeriya ba ta fara samun sauyi ba bayan ADC ta hau mulki a 2027
- Ya ce gwamnatin ADC za ta mayar da hankali kan tsaro, ilimi da tattalin arziki, tare da yaki da cin hanci da rashawa
- Amaechi ya kuma soki cire tallafin man fetur, yana cewa ’yan Najeriya ba su amfana yadda ya kamata ba, yayin da ya yi kira ga gyaran tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan salon mulkin da za su yi.
Amaechi ya ce zai yi murabus idan Najeriya ba ta sauya ba cikin shekara guda na mulkin ADC bayan sun yi nasara.

Source: Twitter
Amaechi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Democracy Today na AIT, inda ya ce gwamnatin ADC za ta ba tsaro, ilimi da tattalin arziki muhimmanci.
Muhimmin ɓangaren da ADC za ta yaƙa
Ya ce yaki da cin hanci da rashawa zai kasance muhimmin bangare wajen magance matsalolin kasar, saboda ana karkatar da kudaden gwamnati zuwa aljihun wasu.
Ya ce dole ne a magance matsalolin tsaro, ilimi da tattalin arziki, yana mai cewa rage cin hanci zai samar da kudaden gudanar da wadannan fannoni.
Amaechi ya kuma soki cire tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi, yana cewa ’yan Najeriya ba su amfana sosai da matakin ba.
Ya ce yana mamakin yadda ake gudanar da shagulgulan almubazzaranci a wasu wurare, alhali talauci ya yi kamari a kasar, cewar Vanguard.

Source: Twitter
Amaechi ya magantu kan tattalin arzikin Najeriya
Amaechi ya ce wani lokaci kan shafe ‘yan mintoci kadan a irin wadannan bukukuwa saboda yana tambayar kansa inda ake samun kudaden da ake kashewa.
Game da tattalin arziki, ya ce Najeriya ta dogara sosai kan shigo da kayayyakin da aka kammala sarrafawa, yana ikirarin cewa sama da kashi 46 cikin 100 ana shigo da su ne.
Ya kuma yi tsokaci kan rahotannin da suka ce wasu ’yan Najeriya sun yi wa Tinubu ihu yayin da ya isa filin jirgin saman Lagos.
Amaechi ya ce idan ADC ta samu mulki, zai yi kokarin ganin Najeriya ta sauya, yana mai cewa mutane za su daina yin irin wannan korafi kan gwamnati.
Ya ce idan Najeriya ba ta fara samun sauyi cikin shekara guda bayan zuwan gwamnatin ADC ba, zai bar mukaminsa.
Abin da zai sa Wike murabus
A baya, an ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana abin da zai saka shi ya yi murabus daga mukaminsa a gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Wike ya ce zai sanar da murabus dinsa ranar 17 ga Janairun 2027, idan Tinubu bai samu nasara a Abuja da Rivers ba a zaɓen shugaban ƙasa.
Ministan ya bayyana cewa yana jagorantar haɗin gwiwar jam’iyyu a Abuja domin samun nasara, tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu.
Asali: Legit.ng

