Gwamnati Ta Bullo da Wani Shiri, Za a Daina Dauke Wuta a Kano da Wasu Wurare a Najeriya
- Gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa kan samar da wutar lantarki ta awanni 24 a kowace rana a Kano da wasu biranen Najeriya
- Gwamnatin ta fara wannan yunkuri ne a karkashin shirin Energy Zones, wanda zai shafi layin wuta na Lagos, Abuja-Kaduna-Kano da Enugu-Port Harcourt
- Gwamnati ta ce wannan shiri zai fi mayar da hankali kan wuraren da bukatar wutar lantarki ta fi yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta fara tattaunawa da kamfanonin raba wutar lantarki kan shirin samar da wuta ta awanni 24 a Lagos, Abuja, Kano da sauran manyan wuraren da bukatar wutar lantarki ta fi yawa a fadin Najeriya.
Shirin da aka kira Energy Zones zai shafi yankin Lagos, hanyar Abuja-Kaduna-Kano da kuma hanyar Enugu-Port Harcourt.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar hutu saboda cikar Najeriya shekaru 66 da samun 'yanci

Source: Twitter
Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya gana da shugabannin wasu kamfanonin rarraba wutar lantarki domin tattauna shirin, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai taimaka wa ministan kan harkokin yada labarai, Adeola Adelabu, ya fitar ranar Laraba.
Gwamnati na kokarin inganta lantarki
Sanarwar ta ce shirin na daga cikin kokarin Gwamnatin Tarayya na samar da ingantacciyar wutar lantarki ga gidaje, ’yan kasuwa da masana’antu a wuraren da bukatar wutar ta yi yawa.
Ta ce shirin zai kuma taimaka wajen magance matsalolin da ke bangaren raba wutar lantarki, tare da tabbatar da cewa wuta da aka samar kuma aka tura zuwa layin lantarki na kasa ta isa ga masu amfani.
Matsalar rarraba wuta a Najeriya
Tegbe ya ce matsalolin da ke addabar bangaren wutar lantarki ba su tsaya kan samarwa da isar da wuta kadai ba.
“Kalubalen bangaren bai tsaya kan samar da wuta da isar da ita ba, har ma ya shafi yawan wutar da ake karba da kuma isar da ita ga masu amfani a bangaren rarrabawa,” in ji ministan.
Ministan ya kuma ce shirin zai iya inganta kudaden shiga da kuma yadda kamfanonin raba wutar lantarki ke karbar kudaden wuta.
Tegbe ya sake tabbatar da shirin Gwamnatin Tarayya na fadada ababen more rayuwa na wutar lantarki a wuraren da bukatar wuta ta fi yawa, yana mai jaddada cewa samar da wuta dole ne ya karu yayin da tattalin arziki ke bunkasa.

Source: Getty Images
Ana sa ran wannan shiri zai mayar da hankali kan wuraren da ’yan kasuwa, masana’antu da sauran bangarorin samar da arziki ke bukatar ingantacciyar wutar lantarki.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana lokacin da za a fara aiwatar da shirin Energy Zones ba. Haka kuma, ba ta bayyana yawan wutar da ake sa ran shiyyoyin za su samar ko irin jarin da ake bukata wajen samar da wutar awanni 24 ba.
Za a kara kudin wuta a Najeriya?
Kun ji cewa Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya warware jita jitar da ake yadawa kan batun ƙara farashin wutar lantarki a Najeriya.
Tegbe ya ce gwamnati ta fi mayar da hankali kan inganta samar da wutar lantarki da kuma ƙarfafa harkar kuɗi da kayan aiki na bangaren wutar lantarki, maimakon ƙara wa masu amfani da wuta wasu kuɗaɗe.
Asali: Legit.ng
