Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutu saboda Cikar Najeriya Shekaru 66 da Samun Yanci
- Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar ranar yancin kan Najeriya
- Matakin gwamnatin na zuwa ne yayin da ke shirye-shiryen gudanar da bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya
- Gwamnati ta bukaci ’yan Najeriya su nuna haɗin kai da kishin ƙasa, tana mai sake jaddada shirinta na inganta rayuwar kowane dan kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta ayyana Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kan Najeriya.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.

Source: Twitter
Gwamnatin tarayya ta bada hutu
Vangaurd ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dakta Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu.
Ministan ya taya ’yan Najeriya da ke gida da ƙasashen waje murnar bikin murnar ranar samun yanci karo na 66.
Tunji-Ojo ya ce karamcin Najeriya, halin karɓar baƙi da soyayya, tare da dumbin arzikin da ke cikin al’ummarta da yalwar albarkatu, sun sanya ta zama “ba tare da shakka ba, ƙasa mafi wadata a tsakanin ƙasashen baƙar fata a duniya.”
Ya bayyana Najeriya a matsayin fitilar da ke haskaka Ajadar Renewed Hope ta Shugaba Bola Tinubu. A cewar ministan, zaman lafiya da kwanciyar hankali “sharaɗi ne da ya zama dole domin ci gaban kowace ƙasa.”
Gwamnati ta ja hankali kan kishin kasa
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi koyi da ubannin ƙasar wajen kishin ƙasa, tare da gina Najeriya irin wadda suke fata, “wadda ’ya’yanmu za su yi alfahari da ita.”
A rahoton Daily Trust, Tunji-Ojo ya ƙara da cewa:

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Ministan tsaron Isra'ila ya dura masallaci na 3 mafi daraja a wurin musulmai
“Yayin da muke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kanmu, ya kamata a ko da yaushe mu tuna cewa akwai fata ga ƙasarmu, kuma bambancin da ke tsakaninmu shi ne ƙarfinmu. Ƙudurinmu na bai ɗaya shi ne ginshiƙin da za a gina ƙasa mai ƙarfi da wadata a kai.”
Tunji-Ojo ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnati za ta tabbatar da samar da Najeriya mafi inganci ga dukkan ’yan ƙasa, a matsayin kyakkyawar girmamawa ga jarumanmu na baya.

Source: Twitter
Ya bukaci ’yan ƙasa su yi amfani da bikin samun ’yancin kai a matsayin damar nuna ƙa’idojin “haɗin kai, kishin ƙasa, zaman lafiya tare da juna da mutunta juna.”
Ya ce Gwamnatin Tarayya “ta ci gaba da jajircewa wajen ƙarfafa tsaron ƙasa, inganta lafiyar jama’a da samar da yanayin da ’yan ƙasa za su iya rayuwa, aiki da kuma cimma halastattun manufofinsu cikin kwarin gwiwa.”
Najeriya ta cimma yarjejeniya da Amurka
Kun ji cewa Gwamnatin Najeriya da Amurka sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin bunƙasa fannin ma’adinan ƙasa a Najeriya.
An rattaba hannun kan yarjejeniyar ne a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, wanda ya gudana a birnin New York na kasar Amurka.
Asali: Legit.ng
