Baya Lashe Zabe, Pantami Ya Sako APC a Gaba, Ya Ce zai Bi Su har Gida Muhawara
- Dan takarar jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa ya shirya yin muhawara da sauran 'yan takara
- Hakan na zuwa ne bayan sake gudanar da zaben fitar da gwani na jam'iyyar PDP da aka yi bayan hukuncin kotu saboda rikicin cikin gida
- A bayanin da ya yi, Panntami ya yi zargin cewa wasu 'yan takara sun fara rokon kar a shirya muhawarar domin kaucewa yin abin kunya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Goombe - Siyasar jihar Gombe na cigaba da daukar zafi yayin da Sheikh Isa Ali Pantami ya sake lashe zaben fitar da gwani na PDP.
Bayan nasara a zaben, Sheikh Pantami ya sake dawo da maganar muhawara da ya nemi 'yan takarar gwamna su gabatar a jihar.

Source: Facebook
A wani bidiyo da Muhammad Bsarky ya wallafa a X, Sheikh Pantami ya sanar da cewa ya kammala shiri kan muhawarar.
Magana kan hukuncin kotu
Sheikh Pantami ya yi zargin cewa wasu 'yan APC na yada farfaganda game da hukuncin da kotu ta yi a kan jam'iyyar PDP.
Ya ce suna sane da komai kuma ba su karya wata doka ba, inda ya ce ana yada maganganu a intanet ne domin kawar da hankalin jama'a.
Batun muhawara a Gombe
Yayin da yake jawabi, dan takarar PDP ya ce sun shirya tsaf domin yin muhawara da sauran 'yan takara domin kowa ya fitoda manufar shi.
Pantami ya ce gayyatar da suka yi wa APC na farko shi ne bayan daya daga cikinsu ya jawo ayar Kur'ani, inda ya ce wani dan takara ya ce shi hafizi ne.
A kan haka Pantami ya ce sun gayyaci duk dan takarar gwamnan da ya ce shi hafizi ne su hallara a wajen da za su yi musaffa.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: An kashe wani shugaban jam'iyyar su Kwankwaso a Arewacin Najeriya

Source: Facebook
A karo na biyu, Pantami ya ce ya kamata a yi muhawara kowa ya bayyana manufofinsa ga al'ummar jihar Gombe.
Sai dai ya yi zargin cewa wasu 'yan takara sun fara kiran kafafen yada labarai da kada su zo jihar muhawara a kan zaben 2027.
A karshe, Pantami ya bayyana cewa ba za su yarda da wani dan takara ya ce ba zai shiga muhawara ba a zaben 2027, inda ya ce suna gayyatar manyan 'yan jarida Gombe.
Ya kara da cewa duk wanda yaki zuwa muhawara dole za a bi har gida domin ya fito ya bayyanawa al'ummar jihar Gombe manufofinsa kafin ya shugabance su.
Ga bidiyon da Pantami ya yi jawabi:
PDP ta dakatar da Mai Lantarki
A wani labarin, kun ji cewa, jam'iyyar PDP a jihar Gombe ta sanar da dakatar mutane biyu da suka shiga zaben fitar da gwani da aka gabatar a ranar Talata.
Mutanen da aka dakatar su ne Khamisu Ahmad Mai Lantarki da kuma Hon. Usman Aliyu Garry kan wasu laifuffuka da jam'iyyar ta ce sun yi.
Tun da farko dai dama Mai Lantarki da Hon. Usman Aliyu Garry sun fito karara sun nuna adawa da samun nasarar da Sheikh Pantami ya yi.
Asali: Legit.ng

