Manyan Labarai A Yau
Aliko Dangote ya bayyana zuba jarinsa a masana’antar masaku a matsayin babban kuskuren kasuwanci da ya taɓa yi a tsawon shekarunsa na harkokin kasuwanci.
Fitaccen jarumin masana'antar fim ta Nollywood da ke Kudancin Najeriya kuma mai shirya fina-finai, Oludotun Baiyewu Jacobs, wanda aka fi sani da Olu Jacobs, ya rasu.
Ƙungiyar Houthi ta ce ta harbo jirgin yaƙin Saudiya kirar F-15 a Yemen da makami mai linzami na kariyar sama da ta kera da kanta. Ta ce za ta ci gaba da kare Yemen.
Da ga shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Nuru Khalid wanda ya yi ridda zuwa Kiristanci ya dawo addinin da ya taso a cikinsa. Ya nemi afuwa.
Hamshakin attajiri, Aliko Dangote ya ce fasa-kwaurin man fetur zuwa ƙasashen makwabta na taimakawa wajen tsadar fetur a Najeriya saboda bambancin farashin man.
Aliko Dangote ya ce samun ɗa namiji da zai gaji daular kasuwancinsa ba shi ne fifikonsa ba, yana mai cewa ’ya’yansa mata uku za su iya jagorantar Dangote Group.
Shugaban Kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya ce wadanda suka zuba jari tare da rike hannayen jarin matatarsa na iya zama miliyoniya cikin shekara daya ko biyu.
Peter Obi ya bukaci Jami’ar Najeriya da ke Nsukka ta fitar da bayanan karatunsa, yana cewa ba ya adawa da binciken cancantarsa gabanin zaɓen 2027.
Kenneth Okonkwo, kakakin yakin neman zaben Atiku Abubakar, ya yi hasashen cewa dan takarar ADC zai lashe dukkan jihohi 19 na Arewa da kuma jihohi uku a Kudu.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari